Rubutun adabi na samun bunƙasa sosai a Nijar – Mrs Sadauki 

Spread the love

“Yadda lamarin aurena ke watsewa da zarar an soma zance ya sa nake kiran kaina matar Sadauki”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU 

A Jamhuriyar Nijar ma ana da marubutan littattafan Hausa na zamani da dama, wasu daga cikinsu har duniya ta shaida ƙoƙarin su, inda suka taka rawar gani a gasar Hikayata ta BBC Hausa. Chamsiya Laouali Rabo, na daga cikin matasan marubuta masu hazaƙa da basirar rubutu mai cike da darussa da yawa. Idan kai mai tsoron karanta labaran aljanu ne ko matsafa da masu ƙungiyar asiri to, ka guji karanta littattafan Chamsiya da daddare, don kuwa gwana ce wajen hira da aljanu da ruƙiyyar cire mayu, amma a cikin hikaya, da labari mai riƙe zuciyar mai karatu. A zantawarta da wakilin Blueprint Manhaja, Abba Abubakar Yakubu, Mrs Sadauki kamar wasu suka fi saninta ta bayyana cewa burinta shi ne ta samu shahara a duniyar rubutu, kuma ta samu damar buga littattafan da take yi a onlayin zuwa bugaggun littattafai na zahiri. 

MANHAJA: Ina son ki gabatar mana da kan ki.

CHAMSIYYA: Cikakken sunana shi ne Chamsiya Laouali Rabo, amma a harkar rubutu an fi sanina da Mrs Sadauki.

Me ya sa ki ka zaɓi sunan Mrs Sadauki a matsayin laƙabinki na rubutu, kina da aure ne? 

Na zaɓi sunan Mrs Sadauki a matsayin laƙabin da nake amfani da shi a rubuce-rubucena ne saboda yadda lamarin aurena yake watsewa da zarar an soma zancen. Sai an yi kamar za a yi sai kuma a fasa. A zuciyata nake sawa ai kam duk wanda ya aure ni Sadauki ne, shi ne mafarin sunan.

Ko za ki gaya mana tarihin rayuwarki a taƙaice?

An haife ni a shekarar 1997 a Jihar Maraɗi ta Jamhuriyar Nijar. Na yi makarantar boko daga matakin firamare a école Soura. A shekara ta 2010 na fita zuwa matakin sakandire, inda na yi shekaru a CEG 3. Bayan na rubuta jarabawar ƙarshe ban samu nasara ba sai aka mayar da ni makarantar kuɗi ta CSP HIKIMA a can na samu nasara na ci jarabawata a 2015. Daga nan ne kuma na ƙetara zuwa wata makarantar horar da ɗalibai a fannin ‘Economie Familiale’ (IPSJAAC). Shekara uku na yi a can kafin na samu takardar shaidar kammala karatu a matakin Diploma, a shekarar 2019. Daga nan kuma sai na fara fafutukar neman aikin gwamnati, garin haka ne kuma na fara kai takarduna wuri-wuri ina ajiyewa da fatan ko Allah zai sa a dace. A haka na faɗa aiki a wani gidan rediyo dake nan Maraɗi wato Sarauniya FM. Sosai na ji daɗin aiki da su don mutane ne masu karamci, sai dai kuma Allah bai nufa zan jima ina aiki da su ba, iya stage na yi.

A fannin karatun Islamiyya kuma, na yi makarantar allo, don kusan zan iya cewa duk wanda yake anguwarmu ya yi makarantar nan ta Malam Rabi’u (Allah ya jiƙansa da rahama) ba zan iya cewa ga shekarar da na fara ba don tun ban san wace ce ni ba yayuna ke zuwa da ni. A shekarar 2011 ne na fita daga nan sai aka saka ni a wata makarantar Madarasatul Tambihul Auladil Musulmin, aji na huɗu aka kai ni ajin ƙarshe wato na biyar bayan an binciki karatuna. A shekarar da aka tsara bikin saukarmu ta Alƙur’ani a wannan shekarar ne kuma nake rubuta jarabawa a makarantar boko, sai abin ya zame min biyu, dole aka yi ba da ni ba. 

A ɓangaren aure kuma har yanzu muna jiran lokaci in Allah ya sa da rai da rabo, kuma in ya na cikin ƙaddarata.

Wanne abu ne ya faru a rayuwarki lokacin tasowarki wanda ya taimaka wajen inganta tarbiyyarki da tunaninki?

Zan iya cewa jajircewar mahaifiyata ce, don yadda take sa ido a kanmu sosai. A kullum muna gida, da zarar mun fita to, wajen karatu ne. A lokacin ƙurciya na ɗauki hakan a matsayin takura, sai yanzu na fahimci gata ne iyaye ke yi mana. Kodayaushe idonta na kanmu, ba ta barin mu je yawo marar kan gado. In ma fitar ce to, mai dalili muke yi. Haka ma, ko wasa da yara ke yi ba a barina sai bayan an ja min kunne don kar na wuce wurin wasan, kuma sai an ƙayyade min lokacin da zan koma gida. Idan na wuce kuma jiki magayi, don har dukana ana yi. Wannan ne ya sa har a yanzu da na mallaki hankalina ina shakkar Mamana, don dole da izininta zan fita, in kuma ta ce a’a, na kan yi haƙuri na zauna. 

Wanne abu ne ya sa ki ka fara sha’awar rubutun adabi?

Abin da sa na fara sha’awar rubutu shi ne akwai wata yayata, a lokacin ta na soyayya da mijin da ta aura. Yadda yake bala’in sonta da nuna mata ƙauna, ita kuma a lokacin ba ya gabanta. Amma a haka ya nace, a ƙarshe har ta kamu da sonsa, yanzu ma ta kai su ga aure. To, yanayin yadda suka gudanar da soyayyar ne ya ban sha’awa, ba zan manta ba har biro da takarda na ɗauka na fara rubutu, ina tambayar shi mijin wasu abubuwa ita ma haka. To, daga ƙarshe kuma sai na watsar da batun, sai bayan ta haihu ne kuma lamarin rubutun ya sake dawo min a rai. Yadda Allah Ya jarrabe ni da mugun son jaririn, sai nake ce mata, “Yanzu ya za ki yi in ki tashi kawai kika ga na sace jaririn na bar miki wasiƙa na ce na ɗauke shi ne na gudu saboda ƙaunar da nake yi masa?” “Sai ki tanadi abin da za ki ce masa in ya girma ya tambaye ki ina ubansa.” Ita ce amsar da ta bani. Ni kuma kamar da wasa na ce, “Sai na ce masa jinina ne kai.” To, daga nan ne fa ko sunan yaron ba a yi ba na dasa alƙalamina.

Ko za ki iya tuna labarin farko da ki ka fara rubutawa?

Labarina na farko da na rubuta shi ne, ‘Jinina Ne Kai’.

Wane ne ya fara koya miki yadda za ki yi rubutu, ko nuna miki ƙa’idojin rubutu?

Wacce ta fara koya mini ƙa’idojin rubutu ita ce Nana Aïcha Hamissou. Don lokacin Hausar da nake yi ba daidaitaciya ba ce. Ita ce ta nuna min yadda zan yi, sannan ta ɗauki alƙawarin yi min gyara kafin na fitar da labarin.

Wacce shekara ki ka fara fitar da rubutunki, kuma kawo yanzu littattafai nawa ki ka rubuta?

A shekarar 2021 na soma rubutun labarin adabi, kuma a gaskiya na manta adadin littattafan da na rubuta, amma dai na san sun fi 30. Wasu ma har na manta su, sannan banda su a ajiye a yanzu. 

Gaya mana sunayen littattafan da za ki iya tunawa, kuma ki yi mana bitar fitattu uku a cikinsu.

Kamar yadda na faɗa a farko na manta da wasu, amma ina iya tunawa akwai, ‘Jinina Ne Kai’, ‘So Ko ƙauna’, ‘Hasken Soyayya’, ‘Abokin Yayana’, ‘Muhammad Kareem’, ‘Ɗan Daba’, ‘Cikin Aljan’, ‘Ciwon So’, ‘Ƙawar Momina’, ‘Bokanya’, ‘Ruhin Aljan’, ‘Farashin Tasiri’, ‘Ƴan ƙungiyar Asiri’, ‘Nata Matar Aljan’, ‘Macijin Ciki’, ‘Ɓoyayyiyar Duniya’, Likitan Mahaukata’, ‘Ɓoyayyen Sirri’, ‘Karuwar Gida’, ‘Mahaukacin So’, ‘Hadeeyatullah’, ‘Seeya’, ‘Toby Ɗan Dambe’, ‘Basheer’, ‘Matar Mahaukaci’, ‘Bango’, ‘Tuzuru’, ‘Sadam’ ‘Sojana’, ‘Mutuware’, ‘Rosella Matsafiya’ da kuma ‘Saurayina’. 

Labarin ‘Mutuware’ na ɗaya daga cikin fitattun littattafaina. Labari ne akan wata maaikaciyar jinya da ba musulma ba, wacce take da ilimin duba, in mutum maye ne ko yana harkar tsafi da zarar ta ganshi za ta iya ganewa. A cikin wannan littafin labarin na yi nuni ne da mutuwar da ake samu ta tsafi wacce kafin wa’adin mutum ya cika sai mayu su kashe shi. To, ita wannan ma’aikaciyar jinyar muddin aka kawo gawar mutum a asibitin da take aiki, ko barci take yi, sai gawar ta yi magana har ta zo kunnenta. Ita kuma sai ta je can sashin ajiyar gawa ta yi hira da matattun da aka ajiye, har a ƙarshe ta je ta yi yaƙin ƙwato ruhinsu wurin mayen da ya karɓe.

Sai littafin ‘Basheer’, shi kuma labari ne akan wani matashin saurayi da yayi nasarar ƙwato wata matashiyar budurwa da mahaifinta ya sadaukar wa ƴan ƙungiyar asiri ita. Tun tana jaririya ƙungiyar ta kafa wa mahaifinta dokar sai ya kusance ta in ta kai wasu shekaru, wannan ya sa mahaifin nata ya killaceta ba ya bari ta kula samari. Ya cusa mata ƙiyayyar maza, kullum mu’amalarta da mata kawai take yi, a dalilin haka ne har ta fara lalata da mata ƴan’uwanta, wanda kuma bai yi nisa ba mahaifinta ya gano halayyar da suke yi, ya kuma illata yarinyar da suke shiriritar. A ranar da wa’adin shekarun da ƙungiya ta ɗibar masa kan zai kusanci ƴarsa sai ya ɗauke ta zuwa wani babban rafi. Kafin ya kai ga cimma burinsa ne Basheer ya ƙwaceta ta hanyar amfani da karatun Alƙur’ani Mai Girma, ya tarwatsa duk wasu dodanni da suka kewayeta.

Shi kuma littafin Bokanya, labari ne tsakanin uwar miji da matar ɗa. Tun da ya auro ta uwar mijin ta tsane ta, wannan ya sa ta dinga tsorata matar ɗan nata, sai ta fito mata a siffar mage ko kuma ta fito cikin wata mummunar kama, a duk lokacin da matar ɗan ta zo gaban madubi. 

Shin kin taɓa buga wani a cikin littattafanki ko duka a onlayin ki ke sakewa?

Ban taɓa buga littafi ba, amma ina da wannan niyyar bugawa, nan gaba kaɗan, in sha Allahu. 

Wacce ƙungiyar marubuta ki ke a Nijar ko a Nijeriya? Kuma wanne taimako ƙungiyar ke miki a rubuce-rubucenki?

Ina Ƙungiyar First Class Writers Association ne, kuma babu shakka ina samun cigaba sosai, don ana koyar da mu dabarun rubutu, sannan in mutum ya yi kuskure a rubutunsa ana yi masa gyara. Muna da jajirtacciyar shugaba, wacce muddin ka yi ba daidai ba to, za ta fito ta gyara maka. Ba na mantawa ta sha yi min gyara, musamman a littattafaina na soyayya, wanda wani sa’in akwai kuɓucewar alƙalami ka rubuta abin da bai dace ba, amma da taimakonta yanzu duk na bar yi.

Waye a cikin marubuta ya zama miki madubin kwaikwayonki, a salon rubutunsa ko gogewarsa?

Marigayiya Hadiza Salisu Sharif ita ce madubin kwaikwayona, domin ina karanta littattafanta sosai, kuma salonta yana burgeni ainun. Zan iya cewa ma har da yawan karantar littattafanta yake ƙara min ƙaimi.

Yaya alaƙarki take da masu bibiyar littattafanki, kuma ta yaya ki ke hulɗa da su?

Ina da kyakkyawar alaƙa tsakanina da masu bibiyar litattafaina, don na kan zauna mu yi raha da zaurukan whatsapp inda nake fitar da littattafaina. Sannan suna bani shawarwari kamar yadda nake basu, in kuma na fitar da littafi na kan saurare su mu kuma fahimci juna dangane da ƙorafe-ƙorafensu. 

Shin wani makarancin littattafanki ya taɓa baki wata shawara da ta sa har ki ka canza wani tsari da ki ka yi wa labarinki?

E, sosai. An sha bani shawara, kuma ina ɗauka. A can farko na faɗa maka na yi aiki a wani gidan rediyo to, akwai wani ɗan jarida Laminou Gonda yana bibiyar littattafaina sosai, a duk lokacin da ya ga wani naƙasu a labarina shi ke bani shawara, wani sa’in ma sai na zo tsakiyar labari, amma a haka zan yi ƙoƙarin juya labarin ya karkata kamar yadda ya bani shawara in na yi hakan zai fi dacewa. Wani sa’in kuma tun a sunan labari zai ce ba hakan ya dace na saka ba, sai kuma na gyara ɗin. Akwai labaran da har na kammala su amma sanadin shawara haka zan zauna na sabunta su na yi musu gyare-gyare.

Yaya ki ke samun jigo ko basirar yin rubutunki?

Ina samun jigo ne ta hanyoyi biyu zuwa uku. Na farko hoto mai motsi kamar a fim. Da zarar na ci karo da wani hoto sai na ji na samu jigo kamar littafin ‘yan ƙungiyar asiri da na rubuta shi ma ta hanyar wani hoto na samu jigon shi. Sai hanya ta biyu, nakan tsaya na yi nazari mene ne ya fi damun al’umma ko yake ci musu tuwo a ƙwarya, kamar littafina na Saurayina, wanda na yi duba ne ga yadda ƴammata a yanzu suke wahala akan son wanda bai damu da su ba. A ƙarshe kuma ina samun jigo ta hanyar hiraraki walau a rediyo,ko facebook ko dai wani abu makamancin haka.

Wanne littafi ne rubutunsa ya fi baki wahala, kuma wanne ne ya fi miki saukin kammalawa, mene ne dalili?

Littafin da ya fi bani wahala wurin rubutawa shi ne ‘Kabewar Kan Kabari’, saboda na yi shi ne bisa jinsi biyu, mutane kuma da aljanu. Na yi bincike sosai game da shi don sai da na zaƙulo ayoyi masu karya sihiri da hana tasirinsa. Haka kuma, littafin da ya fi min sauƙi shi ne na ‘Mutuware’, saboda tun kafin na fara rubuta shi sai da na zauna na yi nazarinsa tun daga farko, tsakiya da kuma ƙarshe.

Yaya harkar rubutun adabi take a Jamhuriyar Nijar, shin ana samun marubutan Hausa sosai kuwa?

Zan iya cewa kam rubutun adabin Hausa yana samun bunƙasa sosai a Jamhuriyar Nijar, don a kullum ana samun cigaba, ta yadda sabbin marubuta ke fitowa.

Su waye aminanki da ku ke zumunci sosai a cikin marubuta?

Marubutan da muke zumunci sosai su ne Hajiya Maryam Sakatare, Rahinatou Mamadou, Princess Aishatou, Ameera Adam, Sadiya Abdulrazak, Mss Flower, Sajida Nijar, da Autar Manya.

Shin tun bayan fara rubutunki na kanki, kina samun damar karanta littattafan wasu marubutan?

E, ina karanta littattafan wasu marubutan, amma ba irin sosai sosai ɗin nan ba. Na fi mayar da hankali kan karatun littattafan Faranshi.

Yaya ki ka koyi rubutu da Hausar Ingilishi a maimakon rubutu da turancin Faranshi da ku ke amfani da shi a ƙasarku, har ga shi kin zama marubuciya?

A makarantunmu na Nijar ai ana koyar da Ingilishi, don haka wannan ba zai zama abin mamaki ba, sannan duk da ban wani ƙware ba, amma in aka yi ina fahimtar abin da ba a rasa ba. Wani sa’in kuma na kan yi binciken wasu kalmomin daga Hausa zuwa Ingilishi don fahimtar da masu bibiyata, kasancewar ƴan Nigeria sun fi yawa.

Wanne buri ki ke da shi nan gaba a harkar rubutun adabi?

Babban burina shi ne na shahara sosai ta yadda duniya za ta san ni fiye da yanzu. Sannan ina da burin buga littattafaina ta yadda zan dinga ganinsu a gabana a ajiye. A ƙarshe kuma ina da burin kai su gidajen rediyoyi ana karanta su.

Kina da wata shawara ga marubutan Hausa na Nijar, kan yadda za a ƙara samun haɗin kai da rubutu masu inganci?

Shawarata ga marubutan Nijar da duk ma wasu marubutan shi ne mu haɗe kanmu mu zama tsintsiya guda. Banda nuna ƴan’ubanci, da nuna ni na daɗe a harkar rubutu don haka ba zan yi mu’amala da masu tasowa ba. Ina kira a gare su da su sanyayya zukatansu don kowa daga nan ya fara, kar kuma ruwan zafi ya manta lokacin da yake na sanyi. Sannan mu inganta rubutunmu ta yadda mutane za su amfana da shi ba wai don nishaɗi ba,duk rubutun da mutum ya san babu darasi ko abin da za a tsinta barinsa shi ya fi alkhairi gare mu ga kuma al’umma.

Kin taɓa shiga gasar marubuta, kuma wacce nasara ki ka samu?

Na taɓa shiga gasar Hikayata ta BBC Hausa a shekarar 2022 da kuma 2023 sai dai dukkansu babu wacce na yi nasara. Gasar da na taɓa ci, guda ɗaya ce wacce ƙungiyarmu ke shiryawa ta gwarzon labarin wata-wata, inda na zo ta ɗaya, da labarina mai suna ɗan’daba.

Wacce nasara ko wani abin alheri ki ka taɓa samu ta dalilin rubutu da ba za ki manta da shi ba?

Nasarar da na samu akan rubutu ita ce haɗuwata da mutanen kirki mabambanta a ƙasashe daban-daban. Abin da kuma aka yi min wanda ba zan taɓa mantawa ba shi ne lokacin da aka yi min tiyata wata daga cikin masu bibiyar littattafaina ƴar Nijeriya, mai suna Zulfa’u Yahaya ta yi tattaki ta zo har Nijar, domin ganina ta kwana ɗaya a gidanmu sannan ta koma. Abu na biyu kuma shi ne a shekarar nan akwai wata mai bibiyar littattafaina da ta ji na je can jahar su ta Yamai wurin bikin ƴar’uwata da ta haihu, haka ta zo inda nake har da kawo min, na ji daɗi sosai matuƙa.

Wasu marubuta kan ce suna rubutu ne don faɗakarwa, wasu suna yi don nishaɗantarwa, wasu kuma su ce su don neman kuɗi kawai suke yi. Ke don me ki ke yin rubutu, mene ne dalilanki?

Ina yin rubutu don manufofi da dama, don na faɗakar. Saboda kusan labaraina za ka same su da manyan darussan rayuwa da kuma amfani ga al’umma. Sannan kuma ina yi don kasuwanci ba tare da jin kunya ko ɗar ba zan ce rubutu ya zame min jari, don wayar hannuna ma da nake rubutu da ita, da kuɗin rubutu na saye ta. Sannan na kan yi rubutu don nishaɗi musamman in na samu kaina a halin kewa yin rubutu yana gusar min da kaɗaici. Ina jin daɗi in na shiga zaurukan marubuta in ga ana ta yi sharhi sunana na yawo

Shin kina sha’awar rubutun wasan kwaikwayo ko waƙoƙi?

Ina sha’awar yin waƙa tabbas, don ko a yanzu wani sa’in ina zauna nakan rubuta, musamman in ina cikin shauƙi haka zan tsaya na tsara baitukan ƙauna na rera wa saurayina.

Wacce karin magana ce ke tasiri a rayuwarki?

Karin maganar da ta fi yin tasiri a rayuwata ita ce, “Komai ya yi farko zai yi ƙarshe!” Gajeruwar magana ce amma mai ma’anoni da yawa, a ta kowacce irin siga ko rayuwa tana hawa. In mulki ne, ciwo, damuwa da dai sauransu. In ka ɗorata a ma’aunin su duk za ta yi daidai.

Mun godiya sosai 

Ni ce da godiya sosai.

By ukarofi