Yadda Kwankwaso ya juya wa gayyatar EFCC baya

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Kwankwaso, ya ƙi amsa gayyatar da hukumar EFCC ta yi masa a makon jiya don amsa mata tambayoyi.

EFCC ta gayyaci Kwankwaso ne don ya amsa mata tambayoyi kan zargin da aka yi masa na amfani da ofishinsa wajen aikata ba daidai ba, karkatar da kuɗaɗen jiha, nauna rashin adalci wajen rabon gidajen gwamnati a lokacin da yake riƙe da kujerar Gwamnan Kano.

A cewar majiyar MANHAJA, a ranar Alhamis da ta gabata EFCC ta buƙaci Kwankwaso ya bayyana a babban ofishinta da ke Abuja amma ya yi biris.

Jaridar Platinum Post ta rawaito cewa, duk ƙoƙarin da aka yi don jin ta bakin Kwankwaso kan wannan batu hakan ya ci tura. Tare da cewa, wata majiya ta kusa da EFCC ta ce akwai yiwuwar EFCC ta cafke Kwankwaso matuƙar ya ci gaba da ƙin amsa mata gayyata.

Gayyatar tsohon gwamnan ta samo asali ne tun a 2015 sakamakon ƙorafin da ƙungiyar ma’aikata ta Concerned Kano State Workers da kums masu karɓar fansho suka yi, inda suka zargi Kwankwaso da take Dokar Fanshon Jihar Kano ta 2007 tare da saɓa ƙa’idar miƙa kuɗaɗen fanshon da aka zabtare wa ma’aikata tsakanin 2011 zuwa 2015 wanda ya kai Naira biliyan N10.

Idan za a iya tunaws, Kwankwaso ya yi gwamnan Kano daga 2011 zuwa 2015, da kuma 1999 zuwa 2003.

A cewar masu karɓar fansho, Kwankwaso ya ba da umarnin a yi amfani da kuɗaɗen fansho wajen samar da gidaje wanda galibi aka ce masu karɓar fansho ɗin ne za su fi cin moriyar shirin.

Amma a ƙarshe Kwankwaso ya yi amfani da ƙarfin ikonsa wajen jirkita yarjejeniyar da aka cimma inda ya raba gidajen ga hadimansa da makusantansa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *