Yadda mutuwar Jarumi Kamal Aboki ke shirin sauya akalar rayuwar matasa

Daga AISHA ASAS

A ranar Litinin, 16 ga wannan watan ne labarin mutuwar jarumin barkwanci Kamal Aboki ta yi dirar mikiya a tsakanin kafefen sada zumunta da kuma masana’antar fim ta Kannywood, sakamakon kasancewar mutuwar ta fuju’a, wato ba-zata.

An ruwaito cewa, Kamal ya mutu ne sakamakon hatsarin mota da ya yi a hanyar Maiduguri zuwa Kano.

Wannan mutuwa ta matashi Kamal Aboki da ke tsaka da cin gajiyar lokacinsa ta ɗaga hankalin ‘yan ciki da wajen masana’antar Kannywood.

Za ka amince da hakan idan ka yi duba da yadda kafafen sada zumunta irin su Facebook, Instagram da kuma TikTok suka tsaya cak na ɗan lokaci, ba abin dake amo face labarin mutuwar matashin.

Idan muka ɗauki kafar TikTok wadda ta yi ƙwaurin suna ta hanayar yawaitar matasa mata da maza dake aikata ababen fitsara da sunan wayewa. Da yawa daga cikin masu wannan aikin sun bayyana mutuwar Kamal a matsayin abin da ya dake zuciyarsu, ya sanya masu tsoron rayuwa.

Wasu daga cikinsu sun fitar da bidiyo suna kuka yayin da suke nuna alhini tare da girgiza da mutuwar ta ‘kun fa ya kun’ da jarumin na barkwanci ya yi, wadda ta sa su tunanin yaushe tasu za ta zo, kuma a wane yanayi za ta riske su.

A ɓangaren kafar Facebook ma ba a bar su a baya ba, wurin nuna alhini da yabon mamacin tare da bayyana irin kyawawan halayarsa. Da yawa sun bayyana mutuwar a matsayin dalilin da zai sa su bar abinda suke aikatawa da ba daidai ba, sakamakon tunanin su ma hakan za ta iya kasancewa gare su.

Wani matsahi da na ci karo da rubutunsa a kafar Facebook ya kira mutuwar jarumin a matsayin silar shiriyar matasa da yawa, inda ya saka hoton rubutun wani matashi a wani zaure da aka buɗe don labaran batsa, yaɗa bidiyo da hotuna na batsa da kuma haɗuwa da abokan shashanci mai suna ‘Gidan Harka’.

A rubutun matashin mai suna Sani Y. ya ce, “Assalamu alaikum. Ina neman yafiyar duk wanda na vata wa rai a wannan gidan, wallahi mutuwar bawan Allah nan Kamal Aboki ta tsaya min arai sosai. Allah ya ba mu ikon barin wannan rayuwar kafin mutuwa ta riske mu. Ni dai in sha Allah zan bar gidan nan.”

Ta ɓangaren malamai ma an samu wasu daga ciki da suka yi amfani da wannan taushi da mutane suka yi don qara nusar da su hanyar gaskiya tare da tsoratar da su makomar wanda ya mutu bisa hanyar varna.

Allaha Ya jiƙan Kamal, Ya gafarta masa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *