Kotu ta bai wa DSS umarnin gurfanar da Tukur Mamu ko ta sake shi

Daga WAKILINMU

Babbar Kotun Jihar Kaduna ƙarƙashin Mai Shari’a E. Andow, ta umarci hukumar tsaro ta DSS da ta gurfanar da Tukur Mamu ko kuma ta sake shi tare da wani mutum da take tsare da su.

Umarnin na kotu na ƙunshe cikin takardar da aka raba wa manema labarai mai ɗauke da lambar ƙara KDM/KAD/1442/2022.

Waɗanda lamarin ya shafa sun haɗa da Tukur Mamu, Faisal Tukur Mamu, Ibrahim Hussain Tinja, Abdullahi Mashi, Mubarak Hussain Tinja da kuma Yahaya Bello.

Yayin da DSS da Babban Lauyan Tarayya su ne waɗanda umarnin kotun ya rataya a wuyansu.

Yayin zaman kotun, Mai Shari’a E. Andow ya ce tun 15/12/2022 waɗanda ke tsare suka nemi kotun da ta ba da umarnin a kiyaye musu ‘yancinsu kamar yadda sassa na 34, 35, 36 da 41 na Kundin Tsarin Mulki na 1999 suka nuna da sauransu.

Sun kuma bauƙaci kotu ta ba da umarnin a gaggauta gurfanar da su a kotu don yin shari’a, ko kuma ba da belinsu kafin lokacin da za a kammala bincike a kansu (idan akwai).

Lauyan Tukur Mamu, Barista M. S. Katu (SAN), ya shaida wa kotun cewa SSS ta saki mutum na 2 da 3 da na 4 amma ban da na 5 da 6.

Barista M.S. Katu ya yaba wa SSS tare da buƙatar kotun ta amince da sakin Mubarak Hussain Tinja da Yahaya Bello.

Idan ba a manta ba, Tukur Mamu, wanda shi ne mawallafin Jaridar Desert Herald kuma hadimin Sheikh Ahmad Gumi kan sha’anin yaɗa labarai, an tsare shi ne a Babban Filin Jirgin Saman Malam Aminu Kano bayan dawowa daga ƙasar Masar kuma ya yi nufin zuwa Umarah a Saudiyya.

Tukur Mamu ya kasance mai shiga tsakani wajen tattaunawa da ‘yan bindiga wajen sako fasinjojin jirgin ƙasan Abuja/Kaduna da aka kai wa hari ran 28 ga Maris 2022.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *