Gangamin APC a Bauchi ya gamu da cikas, Buhari da Tinubu ba su yi jawabi ba

Daga WAKILINMU

Taron yaƙin neman zaɓen shugabancin ƙasa na Jam’iyyar APC a Jihar Bauchi ya gamu da cikas sakamakon ɗaukewar wutar lantarki da kayan amsa-kuwa.

Wannan ya sa taron ya gudana ba tare da jin abin da masu ruwa da tsaki da suka samu yin jawabi a wajen taron ke faɗa ba

Wannan matsalar in ji majiyarmu, ta faru ne saboda akasin ɗaukewar na’urorin magana sakamon ɗaukewar wutar lantarki.

News Point Nigeria ta ruwaito cewa, har aka waste taron wanda ya gudana ranar Litinin a Filin Wasannin Motsa Jiki na Abubakar Tafawa Ɓalewa, Bauchi, Shugaba Buhari da ɗan takarar shugabancin ƙasa na APC, Sanata Bola Ahmad Tinubu, ba su samu zarafin cewa komai ba.

Wata majiya daga tawagar APC ta faɗa wa majiyarmu cewa Buhari da Tinubu ba su samu gabatar da jawabi a wajen taron ba saboda kasa shawo kan matsalar da ta auku har aka watse taro.

News Point Nigeria ta kalato matsalar ta fara ne bayan da wutar lantarki da na’urorin magana suka ɗauke.

Kuma jim kaɗan bayan wutar ta dawo har ma Shugaban APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu ya fara jawabi, sai wutar ta sake ɗaukewa, kuma daga wannan lokaci ba a sake jin komai ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *