Magidanci ya kashe matarsa kan cinye masa burodi

Wani magidanci ya kashe matarsa ta hanyar lakaɗa mata duka.

Mutumin mai suna Wilson Uwaechina rahotanni sun ce ya kashe uwargidan ta sa ce mai suna Ogochukwu Anene saboda burodi.

Bayanai sun ce marigayiyar ’yar asalin ƙauyen Umuokpu da ke yankin Ƙaramar Hukumar Akwa a Jihar Anambra, tana auren mijin nata ne mai suna Wilson Uwaechina daga jihar Enugu.

Shaidun gani da ido sun ce tun farko rikici ya kaure tsakanin ma’auratan biyu ne akan gutsirin burodi.

Mahaifiyar marigayiyar ta shaida wa manema labarai cewa, mista Wilson Uwaechina ya cinye gutsirin burodi da ta sayowa ’ya’yansu ne bayan da ta tambaye shi dalilin da ya sa ya cinye sai kawai ya hauta da duka wanda sanadiyar haka ta rasa ranta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *