Zan rushe duk wani gini da aka yi a jikin badala idan na zama Gwamnan Kano – Dawisu

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Ɗan takarar Gwamnan jihar Kano na jam’iyyar PRP, Salihu Tanko Yakasai da aka sani da Ɗawisu, ya bayyana cewa idan ya samu damar zama Gwamnan Jihar Kano zai rushe duk gine ginen da aka yi a jikin Badala a jihar.

Salihu ya bayyana hakan ne yayin da yake amsa tambayoyi a muhawarar ‘yan takarar Gwamna da ya gudana a ranar Lahadi a gidan Munbayya da ke Kano.

Taron wanda Jami’ar Bayero da haɗin gwiwar wasu ƙungiyoyi masu zaman kansu suka shirya ya samu halarta kusan mafi yawan ‘yan takara na jam’iyyu daban-daban a Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *