Ni’imarki, darajarki (1)

Daga AISHA ASAS

Ni’ma na ɗaya daga cikin halittun da Allah ke yi waɗanda ke iya ƙaruwa ko raguwa, kuma ba a haramta ki nemi ƙarin ta ba matuƙar kin bi hanyoyi da suka dace.

Abin haushi da takaici, a wannan zamanin ba abin da mata suka sa wa gaba face neman aljihun miji ko mallaka, ki dinga juya shi kamar waina.

Wannan shi ne dalilin dake tsunduma mata da dama a halaka da sunan neman maganin ƙarin ni’ima, sakamakon ido rufe suke karɓar duk abinda aka zo masu da shi, matuƙar da sunan ni’ima ce.

Idan kina cikin jerin waɗannan mata, wannan shafi na yau ba naki ba ne, domin Asas na magana ne da matan da suke son ƙara ni’ima don kwanciyar hankalin mazajensu, waɗanda ke so su ba wa mazajensu natsuwa, su kawar da sha’awar matan banza a ransu. Idan kina ciki zance ki biyo ni don muga abin da zai ture wa buzu naɗi.

‘Yar uwa akwai hanyoyi cikin sauqi da za ki mallaki mijinki, ya dinga bauta miki ba tare da sanin ya zama bawa gare ki ba, har a fara tsegumin kin mallake shi.

A wannan shafi na yau zan yi magana ne a kan ɗaya daga cikinsu, wato ‘iya gado’. Idan ya haɗu da wadatacciyar ni’ima zai zama makamin da zai iya yaƙar ko wane juyayyen namiji.

Sau da yawa mata mu ke disashe ni’imarmu ta hanyar ƙin kula da farjinmu.

Ki sani ya ke ‘yar uwa, farjinki na buƙatar kulawar ki fiye da kowanne ɓangare na jikinki. Ki kare shi daga dauɗa, ki tsaftace shi, sannan ki tarairaye shi, domin shi ne darajarki.

Sannan yana da kyau ki ilimintu da wani abu da muka maida ba komai ba, amma yana da illa a lafiyar farji.

A lokacin da ki ka kusanci maigidanki, mata da yawa sukan gyara kwanciya ne su yi barci ba tare da sun damu da tsaftace gabansu ba, hakan kuwa yana daqile ni’ima kuma yakan haifar da warin gaba.

Hanyar da zata tseratar dake kuwa ita ce, ki daure ki tashi, ki samu ɗan ruwan ɗumi ko da ana zafi, idan za ki yi masa gata kuwa sai a surka ruwan da ɗan jiƙaƙƙen Kanumfari da ɗan miski a tsarkake wurin da su ko da kuwa ba za ki yi wanka a lokacin ba. Wannan haɗin zai kashe ƙwayoyin cuta da za su iya daƙile miki ni’ima.

Kuma idan ya bi jikinki to fa ko da maigida zai ƙara zagaye ba tare da kin miƙe ba ba zai ji ɗan bashi-bashin fitar maniyi ba.