Sai an samu ingantaccen tsari FACAN za ta yi nassara a Nijeriya – Alhaji Husaini

Daga MUHAMMADU MUJJITABA a Kano

Alhaji Hussaini Saleh Ahamad, Shugaban Ƙungiyar Masu Ƙungiyar Fitar da Kayan Albarkatun Gona daga Nijeriya na Ƙasa (FACAN) ya ce, tsarin nan na ‘commodities and export Department’ (CID) da ake ƙoƙarin mayar da shi ta hanyar fasahar sadarwa ta zamani ba zai yi nasara ba sai an samu ingantaciyar wutar lantarki da ingantaciyar hanyar sadarwa ta zamani wato sabis sanan shirin zai samu kyakyawar nassara a Nijeriya.

Shugaban ƙungiyar masu futar da amfanin gona da sauran kayayyakin waje shi ne ya bayana haka a lokacin bitar yini guda da ma’aikatar ciniki da masana’antu ta shirya wa ‘yan kasuwar kan yadda za su zamanantar da hada-hadar kasuwancinsu ta hanyar intanet ya ce, akwai buƙatar samun wadataciyar wutar lantarki a Nijeriya kafun ace wannan tsari na E-commerse ya samu nassara a Nijeriya.

Haka kuma shugaban Husaaini Saleh Ahamad na FACAN, ya shawarci gwamnatin Tarayya da na jihohin kansu su ƙara ƙoƙari wajen samar da tsaro da inganta harkar kasuwanci ta yadda muta ne da dama daga sassa daban-daban na duniya za su zo su zuba jarinsu a Nijeriya, wanda hakan zai ba miliyoyin matasa aikin yi inda kuma ya yaba wa ma’aikatar ciniki da masana`antu ta Nijeriya, da ta shiryawa masu futar da kayayyakin amfanin gona wannan bita ta yini guda a kano wanda Musa Audu, ɗaya daga cikin jam’an ma’aikatar ya jagoranta a Kano.

A ƙarshe, babban jami`i mai kula da harkar albarkatun noma da ake futarwa da su bisa tsarin doka ya ce, maƙasudin wannan bita shi ne a wayar da kan masu wannan sana’a ta yadda zata yi daidai da zamani yadda zasu ci albarkacin fasahar sadarwa a Nijeriya, inda ya qara da cewa ba shakka wannan tsari da CED ta zo da shi na buƙatar samar da ingantatun hanyoyi masu kyau da kyakyawan tsari na riga riga da sufuri tun da ya san gwamnatin Tarayya na iya ƙoƙarinta na ganin wannan tsari ya samu nassara a Nijeriya, dan bunƙasa tatalin arziƙin al’umma da ƙasa baki ɗaya.