Ƙungiyar Masana Harkar Gini sun gudanar da taron shekara a Kano

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Ƙungiyar Masana Harkar Gine-gine na Ƙasa (NIOB), reshen Jihar Kano, sun gudanar da taron shekara.

Shugaban ƙungiyar, Alhaji Muhammad’ Sa’ad Umar ya ce, taron na shekara ne kamar yanda dokar qungiyarsu ta ƙasa ta tanada don a wayarda kan mutane sannan kuma a ƙarawa juna sani akan abinda ya shafi sabbin abubuwa da ya shafi gini.

Sannan kuma a tattauna babbar matsalar dake ci musu tuwo a kwarya ta rushewar gine-gine a ƙasar nan gaba ɗaya musamman jihar Kano.

Alhaji Muhammed Sa’ad Umar ya bada misali da cewa akwai gini da ya rushe na kan titin Bairut kwanannan. Kuma babban matsalar da ke jawo rushewar gini shine na rashin bin ƙa’ida.

Ya yi nuni da cewa da yawa a gini za a fitar da taswira da tsari, amma ba’a shigar da turawan gine-gine masana kuma duk abinda za a shigarda kwararre za’a sami mafita da zai magance rushewar gini. Shi kuma hatsarin rugujewar gini zai jawo asarar rai da dukiya saboda kayan ginin ba kyauta ake ba dashi ba.

Shugaban Ƙungiyar na turawan gini na ƙasa reshen kano. Muhammad Sa’ad Umar ya ce idan dai za a yi amfani da masana za a magance magance rushewar gine-gine kuma zaisa a magance asarar dukiya.

Ya ce daga dalilan da yasa mutane basa neman masana akwai rashin tabbatar da tsarin daga Gwamnati domin kamata ya yi ace duk gininda za’ayi a jihar Kano ko a ƙauye mutum yake, ko gona za a fitar sai an fitar da hanya, saboda ita hanya dole ce mota zata wuce ko wacce ma za ta kawo kayan gini ne, amma sai a rufe hanya wasu kuma a unguwanni sai a yi matattarar bahaya na gida a waje ta tare hanya saboda rashin bin ƙa’ida.

Muhammad ya ce duk da cewa akwai dokar tsara birni amma ba’a ɗabbaƙata, in ana ɗabbaƙa ta mutum zai san in ya saɓa, aka zo aka tarar yana wannan aikin Gwamnati zata ɗau mataki na cin tararsa da tsai da aikin, sannan za a iya kwace fulotin ma ya danganta da matsayin laifin mutum.