Daga DAUDA USMAN a Legas
A ranar Lahadin da ta gabata ne al’ummar Musulmin Shagamu da na Jihar Ogun bakiɗaya suka gudanar da taron addu’ar kwana bakwai da rasuwar babban malamin nan na jihar Ogun Marigayi Malam Gambo Shehu Waddu Shagamu.
Marigayi Malam Gambo Shehi Waddu Shagamu ya rasu ne a Shagamu sanadiyuar ‘yar taƙaitacciyar rashin lafiya.
Kafin rasuwarsa shine na’ibin limamin babban masallacin Juma’a na garin Shagamu, kuma ya rasu yana da shekaru sittin da shida, ya rasu ya bar mata biyu da ‘ya’ya 16, maza shida mata goma.
A cikin ‘ya’yan nasa maza akwai babban ɗansa Muktar Hassan Gambo Shehu Waddu wanda shi ma yana ɗaya daga cikin manyan malaman Shagamu. Tuni dai aka riga da aka yi jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Taron gudanar da addu’ar ta kwana bakwai da rasuwar marigayin ya samu halartar waɗan su daga cikin manyan malaman jihar Ogun da Legas da na sauran waɗansu jihohin Arewacin Nijeriya baki ɗaya, kuma taron addu’ar ya gudana ne a ƙarƙashin jagorancin mai martaba Sarkin al’ummar Hausawa mazauna garin Shagamu Alhaji Garba Inuwa da mai martaba Sarkin Hausawan Abeokuta Alhaji Hassan Hassan kuma shugaban majalisar sarakunan Hausawa mazauna jihar Ogun gaba ɗaya da ƙanin marigayin Khalifa Hassan Waddu da sauran makamantansu.
Tun da farkon buɗe taron addu’ar aka ummurci waɗansu daga cikin malaman da suka samu halartar taron damar karanto waɗansu daga cikin ayoyin Alƙur’ani mai tsarki tare da addu’o’in nemar wa marigayin rahama wajen Ubangiji da shi da sauran Musulmin da suka rigayemu gidan gaskiya.
Mai martaba Sarkin Hausawan Shagamu Alhaji Garba Inuwa yana ɗaya daga cikin makusantan Marigayi Shehin malamin ya bayyana alhininsa dangane da rasuwar marigayin tare da faɗin kyawawan halayensa kafin Allah ya karɓi rasuwarsa.
Sarkin ya ci gaba da cewa Marigayin ya kasance mai juriya tare da jajircewa wajen koyar da addinin Musulunci, ya ce sannan ga haƙurin zama da jama’a.
