Rundunar ‘Hunter Group’ tana gudanar da ayyukanta sau-da-ƙafa a Jihar Katsina – AC Salele

Spread the love

Daga DAUDA USMAN a Legas

Mataimakin Kwamanda na Hukumar Daƙile Aikata Miyagun Laifika ta ƙasa wato ‘Hunter Gruop ko kuma Nigerian Forest Security Serɓice a taƙaice reshen jihar Katsina mai kulawa da shiyyar ƙaramar Hukumar Funtuwa, AC Usman Salele Funtuwa ya bayyana cewa a ƙarƙashin jagorancin Kwamandanta na jihar Katsina Murtala Ahmed hukumar tana ƙara samun nasarori a wajen gudanar da ayyukanta na daƙile masu aikata miyagun ayyuka marasa kyau a jihar Katsina da kewayenta gabaɗaya.

AC Usman Salele Funtuwa ya bayyana hakan ne a wata zantawar su ta wayar tarho da wakilin Blueprint Manhaja a Legas dangane da wannan al’amari.

AC Usman Salele Funtuwa ya ce haƙiƙa hukumar ta Hunter Gruop ko kuma Nigerian Forest Security Serɓice a Katsina tana ƙara samun nasarori a wajen gudanar da harkokin aikinta na daƙile masu aikata miyagun ayyuka kamar yadda ya kamata a jihar Katsina.

AC Usman Salele ya cigaba da cewa kaɗan daga cikin nasarorin da hukumar take samu a jihar Katsina sun haɗa da samun nasarar daƙile ɓarayi masu fasa shaguna da satar wayoyin jama’a da masu yi wa ‘yan mata da yara ƙananu da matan aure fyaɗe da sauran masu aikata ayyuka marasa kyau daban-daban irin waɗannan miyagun ayyukan a Jihar ta Katsina.

Hakazalika ya ƙara da cewa ko a kwana-kwanan nan ma hukumar ta samu nasarar cafke waɗan su matasa ɓarayi waɗan da suka shahara a wajen fasa shagunan jama’a da ƙwacen wayoyi tare da samun manyan wayoyi hannun su a ƙaramar hukumar Funtuwa wanda ba a kissima yawan kuɗaɗensu ba da sauran makamantansu, ya ce akan haka yake ganin ya kamata ya ƙara yin kira ga Gwamnatin Jihar Katsina da sauran masu hannu da shunin jihar da su ƙara ƙoƙori a wajan bai wa hukumar isashen haɗin kai da goyan baya domin kwalliya ta cigaba da biyan kuɗin sabulu ta ɓangaren daƙile miyagun ayyuka a jihar Katsina da kewayenta gadaɗaya.

By ukarofi