Wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta ya tayar da ƙura, bayan wani matashi ya shiga zazzafar muhawara da mahaifiyarsa kan wanda ya dace ya zauna a kujerar gaba a mota tsakaninta da matar aurensa.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne yayin da iyalin suka shirya fita zuwa wani ibadar coci, inda aka hango mutumin tare da matarsa, mahaifiyarsa da kuma ’yar uwarsa suna ƙoƙarin shiga mota domin tafiya.
Da aka zo batun shiga motar, mahaifiyar ta yi yunƙurin zama a kujerar gaba, amma ɗanta ya hana ta, yana mai cewa wannan wuri na matar aurensa ne, ba nata ba. Wannan magana ta janyo muhawara mai zafi tsakanin ɓangarorin biyu.
Mahaifiyar ta dage cewa ita ce ta fi cancanta da wannan matsayi, kasancewar ita ce ta haife shi, tana mai cewa bai kamata ya fifita matarsa a kanta ba. ’Yar uwarsa ma ta mara mata baya, tana goyon bayan ra’ayin mahaifiyar kan cewa ya kamata ta zauna a gaba.
Sai dai mutumin ya tsaya kai da fata wajen kare matarsa, inda ya bayyana cewa lokacin da mahaifinsa yana raye, mahaifiyarsa ce ke zama a gaba, amma yanzu lokaci ya yi da matarsa za ta karɓi wannan matsayi. Har ma ya umarci ’yar uwarsa da ta yi shiru, yana mai jaddada matsayinsa.
Mahaifiyar ta ƙi amincewa da wannan hujja, inda ta bayyana cewa idan ba za a ba ta damar zama a gaba ba, to ba za ta bi su tafiyar ba.
Domin kwantar da hankula da kauce wa rikici, matar aurensa ta buɗe ƙofar gaba ta ba mahaifiyar damar zama a wurin, lamarin da bai yi wa mijin daɗi ba. Daga bisani ya nuna rashin jin daɗinsa ga matarsa, yana mai cewa ta ɓata masa rai da ta bari mahaifiyarsa ta zauna a kujerar gaba.
Lamarin ya jawo muhawara a tsakanin masu amfani da kafafen sada zumunta, inda wasu ke ganin matakin mutumin ya dace da tsarin aure, yayin da wasu ke ganin ya kamata ya mutunta mahaifiyarsa fiye da haka.
