’Yan Nijeriya na ci gaba da karɓar rancen manhajoji duk da tsananin kuɗin ruwa – Bincike

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Duk da yawaitar koke-koke kan tsananin ruwa da kuma matsin lamba daga masu bayar da lamuni ta yanar gizo, bincike ya nuna cewa har yanzu ’yan Nijeriya da dama na ci gaba da karɓar bashi daga waɗannan manhajoji domin magance matsalolin rayuwa, kasuwanci da kuma buƙatun yau da kullum.

Rahoton bincike ya bayyana cewa harkar fasahar kuɗi, wato Fintech, na ci gaba da bunƙasa a Nijeriya, inda wasu kamfanonin lamuni ke amfani da halin ƙuncin jama’a wajen jefa su cikin mawuyacin hali ta hanyar bada bashi mai tsananin ruwa. Baya ga haka, ana zargin wasu daga cikinsu da karya dokokin kare bayanan sirri ta hanyar neman bayanai masu muhimmanci kafin su bayar da lamuni.

Abin da ya fi tayar da hankali shi ne yadda wasu masu karɓar lamuni ke shiga wani irin yanayi na bashi, inda suke karɓar wani bashi daga wata manhaja domin biyan wata, lamarin da ke ƙara musu nauyin bashi da damuwa.

Binciken ya nuna cewa akwai sama da kamfanonin fintech da manhajojin lamuni 450 a Nijeriya, wasu daga cikinsu na da lasisi daga Babban Bankin Nijeriya (CBN), yayin da wasu kuma ke aiki ba bisa aa’ida ba.

Tallace-tallacen yaudara:

A kusan dukkanin dandamalin yanar gizo, ana ganin tallace-tallacen lamuni masu jan hankali da ke bayyana kamar suna da sauƙin ruwa. Waɗannan manhajoji na amfani da dabarun zamani wajen kaiwa ga masu amfani da intanet, suna jan hankalinsu da alƙawurran bashi cikin sauƙi.

Sai dai, kwarewar masu anfani da dama ta nuna cewa da zarar mutum ya karɓi bashi daga irin waɗannan manhajoji, zaman lafiyarsa na iya shiga haɗari. Ana yawan fuskantar kiraye-kiraye da saƙonnin barazana idan lokacin biya ya kusa ko aka samu jinkiri.

A wasu lokuta, ana zargin wasu kamfanonin da ƙirƙirar hotunan mutuwar karya, wato obituary, na wanda bai biya bashinsa ba, suna yaɗa shi a kafafen sada zumunta tare da aika saƙonni na ban-kunya ga iyalai da abokai.

Dalilan karɓar bashi:

Wasu ’yan Nijeriya da aka tattauna da su sun bayyana cewa galibi suna karɓar irin wannan bashi ne saboda matsalolin gaggawa.

Wani direban tasi a Abuja, Shehu Abdullahi, ya ce ya karɓi bashi ne lokacin da ɗansa ya yi hatsari mai tsanani da ya buƙaci tiyata cikin gaggawa. Ya ce babu wanda ya taimaka masa, hakan ya tilasta masa karɓar bashi daga manhajoji biyu, lamarin da ya jefa shi cikin wahala wajen biya saboda tsadar ruwa.

Haka shi ma wani ɗan kasuwa, Stephen Adeniyi, ya bayyana cewa bashin da ya karɓa domin farfaɗo da kasuwancinsa ya jawo masa damuwa har ya kamu da hawan jini, yana mai cewa bai taɓa samun kwanciyar hankali ba tun daga lokacin.

Ra’ayin masana doka:

Wani lauya, Atanda Olatunji, ya bayyana cewa yawancin waɗannan bashin ba sa buƙatar jingina, wato collateral, wanda ke sa kamfanonin su ɗora ruwa mai tsanani domin rage haɗarin da suke ɗauka.

Sai dai ya ja hankalin jama’a cewa doka ba ta yarda da cin mutuncin masu karɓar bashi ba, yana mai cewa duk wanda aka ɓata masa suna ta irin wannan hanya na da damar kai ƙara domin neman diyya.

Tasirin talauci:

Malamar makaranta, Regina Akpan, ta bayyana cewa tsakanin ruwa na jefa mutane cikin talauci, inda ta ba da misalin yadda mutum zai karɓi N500,000 amma a buƙaci ya biya fiye da N1.2 miliyan cikin kankanin lokaci.

Ta shawarci jama’a da su guji karɓar irin wannan bashi domin kaucewa shiga cikin matsin rayuwa.

Raunin kulawar gwamnati:

Wani masanin fasaha, Jude Okpara, ya danganta yawan cin zarafin masu karɓar bashi da rashin tsauraran matakan kulawa daga gwamnati, musamman ga manhajojin da ke aiki ba tare da izini ba.

Ya bayyana cewa wasu kamfanonin na amfani da bayanan sirri wajen matsa lamba ga masu bashi, har ma su wulakanta su a bainar jama’a domin tilasta su biya.

Duk da haka, Hukumar Kare Gasa da Kare Haƙƙin Masu Amfani da Kaya (FCCPC) ta fara ɗaukar matakai ta hanyar tilasta rajista ga duk masu bayar da lamuni ta yanar gizo da kuma hana su amfani da hanyoyin cin zarafi.

Ba dole ba ne a karɓi bashi:

Wani ma’aikacin kamfanin lamuni, Iniubong Frank, ya ce ba a tilasta wa kowa karɓar bashi ba, yana mai cewa ya kamata mutane su tabbata za su iya biyan bashin kafin su karɓa.

Ya kuma bayyana cewa kamfanonin da ke da lasisi na hukunta ma’aikatan da ke cin zarafin kwastomomi, saɓanin waɗanda ke aiki ba bisa ƙa’ida ba.

Buƙatar ƙara tsaurara doka:

Masana sun jaddada buƙatar ƙara tsaurara dokoki da tabbatar da bin ka’ida domin kare jama’a daga cin zarafi. Sabbin dokoki sun haramta amfani da bayanan sirri, tuntuɓar iyalai da abokai, da kuma tura bashi ba tare da izini ba.

Sun kuma tanadi hukunci mai tsauri ga kamfanonin da suka karya doka, ciki har da tara mai tsoka da kuma hana su ci gaba da aiki.

A ƙarshe, masana sun shawarci jama’a da su yi amfani da manhajojin da aka amince da su kawai, tare da tabbatar da sun fahimci sharuɗɗan lamuni kafin karɓa, domin kaucewa faɗawa tarkon bashi mai tsanani.

By ukarofi