Yawan ba mace kuɗi na ƙara arziki, inji Dr. Farouk

Spread the love

Wani likita kuma mai tasiri a kafafen sada zumunta, Dr. Farouk Adebiyi, ya jawo zazzafar muhawara a yanar gizo bayan furta wasu kalamai masu ɗaukar hankali dangane da kuɗi, rawar da mata ke takawa, da kuma samun arziki.

A wasu saƙonni da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta, Dr. Farouk ya bayyana cewa maza da ke bai wa mata kuɗi suna da damar samun ƙarin arziki a rayuwa. A cewarsa, karamci ga mata na da alaƙa kai tsaye da samun albarka da wadata.

Ya rubuta cewa, “Yayin da namiji ke ƙara bai wa mace kuɗi, haka arzikin sa ke ƙaruwa. A yau akwai maza da dama da suke samun miliyoyi saboda suna bai wa mata kuɗi. Ku ɗauka daga gare ni — mata albarka ne daga Allah.”

A wani karin bayani da ya sake yi, ya jaddada cewa tun lokacin da ya fara bai wa mata kuɗi akai-akai, ya riƙa samun albarka a rayuwarsa. Ya ƙara da cewa, “Duk lokacin da na samu dama ina bai wa mata kuɗi, albarka tana bin ni daga ko ina. Idan kana son zama mai kuɗi, dole ka riƙa bai wa mata. Mata an halicce su ne don karɓa, maza kuma don bayarwa.”

Sai dai waɗannan kalamai sun haifar da ra’ayoyi mabambanta a tsakanin masu amfani da shafukan sada zumunta. Wasu sun amince da ra’ayinsa, suna ganin karamci ga mata na iya jawo addu’o’i da albarka. Wasu kuma sun soki kalaman, suna masu cewa sun yi tsauri kuma sun yi janariza ba tare da la’akari da bambancin rayuwa da halaye ba.

Wasu daga cikin masu sharhi sun bayyana cewa mace da ake kulawa da ita na iya yi wa mutum addu’o’i masu ƙarfi da za su kawo masa alheri. A gefe guda kuma, wasu sun yi nuni da cewa ba kowace mace ba ce ke kawo albarka, inda suka gargaɗi maza da su yi taka-tsantsan wajen zabar wanda za su yi hulɗa da ita.

Lamarin ya ƙara bayyana yadda irin waɗannan batutuwa da suka shafi kuɗi, soyayya da zamantakewa ke ci gaba da tayar da muhawara a cikin al’umma, musamman a wannan zamani na kafofin sada zumunta, inda kowanne ra’ayi ke samun damar yaduwa cikin sauri.

A ƙarshe, tambayar da ta rage ita ce: shin karamci ga mata na da tasiri kai tsaye wajen samun arziki, ko kuwa ra’ayi ne kawai na mutum ɗaya? Amsar wannan tambaya na ci gaba da kasancewa abin muhawara a tsakanin jama’a.

By ukarofi