Trump ya umarci sojin ruwan Amurka ta karɓe iko da mashigar Hormuz bayan tattaunawar tsagaita wuta ta rushe

Spread the love

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya umarci rundunar ruwan sojin Amurka da ta fara mamaye mashigar ruwan Strait of Hormuz nan take, bayan da tattaunawar tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran ta rushe.

Rahotanni sun nuna cewa tattaunawar zaman lafiya da aka yi tsakanin kasashen biyu ba ta kai ga cimma matsaya ba, musamman kan batun shirin nukiliyar Iran.

Trump ya ce rundunar ruwan Amurka za ta dakatar da duk wani jirgin ruwa da ke shiga ko fita daga mashigar, tare da hana duk wanda ya biya kudin wucewa ga Iran samun kariya.

Wannan mataki na iya kara tsananta rikici a yankin Gabas ta Tsakiya, kuma yana da matukar tasiri ga harkokin man fetur na duniya, domin mashigar na daga cikin muhimman hanyoyin jigilar mai.

By Babaji