Yadda sojojin Nijeriya suka yi galaba kan rundunar Bello Turji a Sakkwato

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

A daidai lolacin da matsalar tsaro ta ta’azzara a Arewa maso Yammacin Nijeriya, rahotanni sun tabbatar da ƙoƙarin da sojoji ke yi na kakkave ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane a jihohin Katsina, Zamfara da Sakkwato, inda rahotanni ke cewa sojojin sun yi nasarar kakkaɓe rundunar kwamandan dajin nan Bello Turji, wanda ya addabi yankunan Sakkwato da Zamfara.

Shaidun gani da ido sun ce babban kwamandan sojin da ke kula da runduna ta 8, Manjo Janar Uwem Bassey ya jagoranci tawagar sojoji tare da manyan jami’an sa a cikin motocin yaƙi sama da 20, waɗanda suka yi wa ‘yan bindigar ƙofar rago, yayin da sojin sama suka taimaka musu da ruwan wuta ta sama.

Bayanan da ke zuwa daga yankin sun ce sojojin sun yi nasarar kashe ‘yan bindigar da dama tare da ƙona matsugunin su, yayin da suka ci gaba da bin sawun waɗanda suka tsere daga ƙauyen domin kaucewa ruwan wutar.

Janar Bassey ya sha alwashin murkushe wadannan ‘Yan ta’addan da suka hana zaman lafiya a yankin tunda ya karvi ragamar jagorancin rundunar samar da zaman lafiya ta ‘Operation Safe Haven’, kuma rahotanni sun tabbatar da cewar da kan sa yake jagorancin sojojin da ke kai harin cikin dazukan jihar.

Jihar Sakkwato dai na ɗaya daga cikin jihohin Arewa maso Yammacin Nijeriya da ‘yan bindiga suka mamaye wasu sassan ta, inda suke kai munanan hare-hare suna hallaka jama’a.

Makwanni biyu da suka gabata, ‘yan bindigar sun kai ƙazamin hari ƙaramar hukumar Sabon Birni, inda suka ƙona wasu matafiya sama da 40 a cikin motar su, abinda ya sake tada hankalin jama’ar Nijeriya baki ɗaya.

Wannan ya sa gwamnan jihar Aminu Waziri Tambuwal ya ziyarci Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, inda ya buƙaci kafa dokar ta ɓaci a wasu yankunan jihar domin daqile ayyukan waɗannan ‘yan bindiga. Kafin ziyarar, gwamnan ya gabatar da ƙorafi akan yadda sojojin suka gudanar da shirin kakkaɓe ‘yan bindiga a Jihar Zamfara ba tare da tsara yadda za su kare masu tserewa daga yankin suna faɗawa wasu jihohi ba.

Tambuwal ya ce wasu daga cikin waɗanda aka tarwatsa a Jihar Zamfara yanzu haka sun kutsa kai cikin jihohin da ke makotaka da su, ciki har da Sakkwato, inda suke kai munanan hare-hare akan fararen hula.