Tunzirin ’yan Arewa kan matsalar tsaro na kan hanya

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Babu irin sunan da ’yan kudu ba su kira ’yan Arewa da shi ba, daga shaguɓe zuwa baƙar magana, da cin fuska, duk don saboda shiru da kawar da kan da suke yi a kan abubuwan da suke faruwa na taɓarɓarewar tsaro a yankin. Har ma za ka ji wasu ’yan Arewan da ke ganin suna da wayewa irin ta ’yan kudu, su ma suna bayyana takaicin su kan irin wannan kawar da kan da nuna halin rashin sanin ciwon kai na ’yan Arewa. Suna ganin hakan a matsayin gazawa da sakaci, ba ma daga talakawa da ke fafutukar tsira da rayuwar su da neman abin da za su sanya a bakin salati ba, hatta ga ’yan siyasa da wakilan al’umma da ke Majalisar ƙasa ba a jin wata ƙwaƙƙwarar magana na fitowa daga bakunan su, kamar dai matsalar ba ta shafe su ba.

A nasu tunanin ’yan Arewa son mulki da son mata kawai suka iya, amma ba su san yadda za su kare ’yancin su ko mutuncin ran ɗan Adam ba. A ganin wasun su, ba mu damu da kare rayukan ’yan uwan mu ba, ballantana har kasha-kashen da ake yi ya dame su. Daga Boko Haram, an koma ta ’yan bindiga masu kashe mutane da gayya!

Idan ka ware koke-koke a kafafen watsa labarai, da guna gunin raunanan talakawa a nan da can, ba ka jin wani gunji ko motsi na musamman da za a ce wata al’umma, wata ƙungiya ko wani basarake ko wani attajiri daga yankin yana gangamin neman ɗauki ga al’ummar wannan yanki, musamman jihohin yammacin Arewa da suka haɗa da Sakkwato, Zamfara, Kebbi, Katsina, Kaduna da Naija har da Babban Birnin Tarayya Abuja, da kuma na baya bayan nan Jihar Filato.

Rayukan ’yan Nijeriya sun zama kamar kiyashi, a harbe, a yanka, ko a kona mutum da rai ya zama ba a bakin komai ba. Kana hanya ba ka tsira ba, ballantana kana cikin gari ko kusa da iyalan ka. Ta’addanci ya zama ruwan dare, da ranar Allah sai matasa ɗauke da makamai su tare hanya su kashe na kashewa, su sace na sacewa, babu fargabar komai, saboda talakawa kowa na tsorace da rayuwar sa, jami’an tsaro kuma sun yi ƙaranci, babu ingantattun kayan aiki, da ƙwarin gwiwar bibiyar vata gari zuwa maɓoyarsu, ko fadar su inda suke shimfiɗa baƙin mulkin da suka ga dama.

Idan muka ce gwamnati ko jami’an tsaro ba sa komai gaskiya ba mu yi musu adalci ba. Babu shakka ana kashe maƙudan kuɗaɗe wajen sayen makamai da tura jami’ai zuwa samun horo da shiga dazuka. Amma alal haƙiƙa matakai da dabarun da ake amfani da su a kan waɗannan ’yan ta’addan sun yi ƙaranci gaskiya, shi ya sa talakawa ba sa ganin tasirin abubuwan da ake yi. A kullum ’yan ta’adda suna nuna gaba suke da jami’an tsaro, wajen dabaru da kai hari a daidai inda suke son kai wa.

Ƙarancin jami’an soja da ƙarancin sabbin makaman zamani a hannun su ya sa duk ƙoƙarin da ake yi na yaƙi da ta’addanci yana tashi a banza a idanun wasu ’yan Nijeriya, saboda ɓarnar da ake yi ta ninka nasarar da ake cewa ana samu. Musamman duba da rayukan da ake rasawa kusan a kowacce rana. Har ta kai ga ana lissafin Nijeriya cikin ƙasashen da ake ɗaukar ran ɗan Adam kamar kiyashi.

Bincike ya yi nuni da cewa, Nijeriya ce ƙasa ta uku a duniya bayan Afghanistan da Iraƙi inda ake kashe rayuka babu laifin tsaye ba na zaune. Wannan ba ƙaramin abin ɗaga hankali ba ne matuqa. Kuma bayan hakan ma nuna halin ko in kula da shugabanni da manyan ’yan siyasar ƙasar ke nunawa, ya ƙara jefa ƙasar cikin halin rashin tabbas.

Ba da jimawa ba, mabiya mazhabar Shi’a a ƙasar nan suka yi makokin bayyana alhinin cika shekaru biyar da kisan kiyashin da sojoji suka yi wa mabiyansu fiye da kimanin 300, saboda zargin ɗaukar doka a hannu da tare hanya a Zariya da ke Jihar Kaduna. A yayin da hakan ke faruwa kuma an ruwaito wasu ’yan ta’adda sun ƙona wasu matafiya fiye da  20 kuma da ransu yayin da suke cikin  tafiya a hanyar Gidan Bawa da ke ƙaramar hukumar Sabon Birni a jihar Sakkwato.

A wata sanarwa da wakilin Majalisar ɗinkin Duniya a Nijeriya Edward Kallon ya fitar dab da ƙarshen shekarar da ta gabata ya bayyana cewa kimanin mutane 110 ’yan ta’addan Boko Haram suka yi wa kisan gilla a rana ɗaya a ƙaramar hukumar Jere da ke Jihar Borno, ciki har da manoma 43 da ke aikin noman shinkafa a gonakinsu.

Labarin kasha-kashen rayuka babu gaira babu dalili a arewacin Nijeriya yana da yawa kuma akwai ban takaici matuƙa. Kai ka ce ba rayukan ’yan ƙasa ba. Talakawan ƙasa na zargin gazawar gwamnati da jami’an tsaro, suna kwatanta yadda ake karrama ran ɗan Adam da na dabbobi a wasu ƙasashen waje. Amma a Nijeriya ba haka abin yake ba, a rubuce ne kawai ake bayyana ɓacin rai da kaɗuwar shugaban ƙasa a duk lokacin da mummunan al’amari irin haka ya faru, amma a aikace ba yadda ’yan Nijeriya suke zato da fatan gani ba.

Mai yiwuwa tunzuri na baya bayan nan da wasu jama’a da ƙungiyoyi daga Arewa suka fara nunawa na fitowa tituna da wuraren shaƙatawa su nuna rashin jin daɗin su da abubuwan da ke faruwa, cikin lumana, tare da aika saƙonnin kira ga mahukunta su yi abin da ya dace, don kawo ƙarshen asarar rayuka da taɓarɓarewar tsaro a Arewa da Nijeriya baki ɗaya, zai taimaka wajen farkar da mahukuntan ƙasar nan su ƙara fahimtar halin da ake ciki.

Abin lura daga bakunan masu shirya wannan zanga-zangar lumana, kalaman su na girmamawa ne ga shugaban ƙasa, domin kuwa ba su yarda an yi amfani da su wajen aibata shi ko kiran ya sauka daga mulki saboda gazawa ba, kamar yadda wasu ke yi a zaurukan sada zumunta da gefen tituna. Amma sun yi amfani da haƙƙin da suke da shi a matsayin su na ’yan ƙasa wajen nuna damuwa ga ci gaban yankin su da ƙasar da suke alfahari da ita.

Tun ba yanzu ba, a kafafen sadarwa daban-daban, ’yan Nijeriya ke jan hankalin hukumomi su ɗauki mataki da wuri kada matsalar ’yan bindigar nan ta kai wani matsayi, irin abin da ya faru da Boko Haram, har a kai yanayin da za su buwayi harkar tsaro da ’yan qasa baki ɗaya. Amma aka riƙa raina abin da za su iya, ana ganin lokaci guda za a iya murƙushe su a gama da su. Tun ba su wuce ƙananan ƙungiyoyi masu ƙananan makamai da ke zuwa fashin dabbobi da kayan abinci ba, yanzu har sun gawurta sun fara ƙwace wani yanki na Nijeriya suna shimfiɗa baƙin mulki da ta’addancin da suka ga dama. Har suna mallakar manyan makaman yaƙi da suke da haɗari kasancewar su a hannun ’yan ta’adda.

A yayin da muke yabawa da ƙoƙarin da hukumomi ke cewa suna yi domin shawo kan wannan matsala, ba dare ba rana, muna ƙara kira gare su, su ƙara zage damtse da aiki da dabarun tattara bayanan sirri, tare da baza jami’an tsaro cikin lunguna da ƙauyuka, don shirin ko ta kwana da kai ɗaukin gaggawa ga mutanen da ke nesa da birane ko da gwamnati.

Sannan ya kamata ’yan siyasa da jami’an gwamnati su fito su nuna damuwar su da ba da shawarwarin da hukumomi za su taimakawa jami’an tsaro kawo ƙarshen wannan musiba. Kuma su nuna damuwar su da gaske kan abubuwan da ke faruwa, a aikace ba a kafafen sadarwa ko a takarda ba kawai. ’Yan Nijeriya na buƙatar ganin sun yi ruwa da tsaki kan al’amarin da ya shafi tsaron lafiyar su da cigaban rayuwar su.

Su ma ƙungiyoyin mata da matasa da ke fitowa don bayyana ƙorafin su ga Gwamnatin Tarayya, muna yaba musu da wannan ƙarfin hali da sadaukarwa da suka nuna, duk da sanin da suka yi na irin abin da zai iya faruwa da su, idan suka ci gaba da taruka ko fita kan hanya da sunan zanga-zanga. Amma bin hanyar lumana da neman izinin hukumomi don ba da kariya kamar yadda doka ta buƙata, zai taimaka wajen jawo hankalin mahukunta da sauran ƙasashen duniya kan wannan matsala.

Haƙƙin ’yan ƙasa ne a ƙarƙashin tsarin dimukraɗiyya su fita titi ko su bi duk wata hanya da doka ta amince da ita, don bayyana damuwar su ko rashin jin daɗi kan duk wani abu da ya ke faruwa a qasa, wanda bai musu daɗi ba ko kuma suke ganin barazana ce ga zaman lafiya da tsaro a ƙasa.

Sai dai aiki da hankali, jajircewa da fitar da ƙudirorin da za a yi zanga-zangar a kai, samar da kyakkyawan jagoranci, da tsari wajen tafiyar da abin da aka sa a gaba, amfani da hanyoyin lumana, don rage zafin tunzurin da wasu ka iya zuwa da shi. Domin hakan ya hana jami’an tsaro ƙoƙarin tarwatsa taron gangamin lumana, ko kuma hana masu kiran shugaban ƙasa ya sauka, ko aibata shi da munanan sunaye.

Shigar masu nishaɗantar da mutane masu shirya fina-finai, mawaka, cikin wannan tafiya, lauyoyi, ‘yan kasuwa, masu ƙwallon ƙafa ya ƙara bayyana irin tasirin da kiran da ake yi yayi. Sai dai kuma kiraye-kirayen bai kamata su tsaya a ɗaukar hoto ana ɗorawa a zaurukan sada zumunta ana ƙwalliya da su ba. Ya kamata a gansu a wajen zaman dirshan ko wajen taron nuna rashin jin daɗi da ake yi, hakan zai yi tasiri sosai

Lokaci ya yi da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai fito ya bai wa ’yan Nijeriya haƙuri bisa abubuwan da suke faruwa na taɓarɓarewar tsaro a ƙarƙashin gwamnatinsa, gwamnatin da ’yan Nijeriya fiye da miliyan 15 suka zaɓa, don bayyana ƙwarin gwiwar da suke da shi, da kyakkyawan fatan ganin rayuwarsu ta samu canji a ƙarƙashin mulkinsa. Ya kuma jajenta musu game da rashe rashen da aka yi na rayukan ɗaruruwan jama’a da aka kashe a sassan ƙasar nan daban-daban musamman ma dai a Arewa, inda kisan gilla ya zama ruwan dare. Da ba su tabbacin ɗaukar matakin da zai kawo ƙarshen taɓarɓarewar tsaro a Arewa a ƙarƙashin mulkinsa.

Sannan ina roƙon jami’an tsaro, musamman ’yan sanda da su bi masu shirya wannan tattaki ko zanga-zangar lumana cikin tsari da ƙwarewa, don gudun samun wasu ƙarin gawarwakin, ko kuma tunzura wasu babu gaira babu dalili su tayar da tarzoma. Ba ma son ƙarin zubar jini a Arewa. YA ISA HAKA!

Allah ya ba mu lafiya da zaman lafiya a Arewa da Nijeriya baki ɗaya.