Yadda bidi’a ke rusa aure

Daga SADIYA GARBA YAKASAI

Sallamu Alaikum warahamatullahi ta’alah wa barakatuhu. Yau ma ga mu da sabon bayani kamar yadda muka saba, a filinmu mai albarka a kan tarbiyya. Muna godiya da ɗimbin masoya masu nuna jin daɗinsu da ba da shawara, ko nuni a kan abun da suke so a faɗakar. Hakan yana sanya mu farin cikin cewa saƙon da muke isarwa yana isa inda ya kamata. Cikin ikon Allah yau ma gani ɗauke da nasiha ga iyaye da amare da angwaye. Kamar yadda wasu bayin Allah suka nuna cewa, don Allah a yi magana akan wannan matsala dake neman rusa aure gabaɗaya.

Taron biki ko suna, waɗannan duk matsaloli ne yanzu masu zaman kansu da ke addabar kowanne jinsi.Ta ina muka fara? ta ina za mu daina? Sai mun taru gabaɗayanmu mun yi wa juna uziri da dubaiyya. 

Mu duba iyaye da kakanninmu. Duba yadda ake bikin aure a da duk ba a san waɗannan abubuwan da yanzu ‘ya’yanmu suka mai da shi ibada ba.

Waɗannan bidi’oin da muka rataya wa kanmu ga su sun  zame mana ƙarfen ƙafa. Wasu daga ciki sun haɗa da:

Bikin suna: Idan mace ta haihu a da komai na al’ada da ake yi  cikin aminci da daraja da kulawa. Za a yi ƙauri, za a yi kunun  kanwa, har a raba wa ma}ota tare da ƙauri. Yanzu duk an daina kayan barka, kayan fitar suna na mai jego su ma an daina, saboda babu ko saboda wahalhalun da aka fito da su lokacin biki. Maza yanzu su ma sun daina. Da, za a jera kwana huɗu ana gasa wa mai jego nama, amma yanzu baiwar Allah sau ɗaya ma idan ta samu ta gode Allah.

Kayan jariri na yaro ba sa samuwa balle a ba wa mai haihuwa nata kawai saboda rashi ko kuma tunanin fitinar da aka yi masa tun lokacin biki. shi ma sai ya toshe bakin aljihunsa ya yi ƙyamas.

Baƙaƙen al’adu da muka ɗebo ya jawo a ce idan an haihu sai an kama guri, sai an yi abinci kala-kala. Idan shi miji bai da wannan damar da me zai ji? wahalar haihuwar ko kuɗin makarantar yara ko kuma sauran buƙatu?

Yana da kyau idan an busa a furzar, saboda raguwa. Yanzu ba irin da ba ce, a yi yadda muka gada mana. A yi komai a gida, a watse. Ba sai maijego ta ɗaga wa mijinta hankali ba.

Bikin aure:Wannan shi ne ƙoluluwar tashin hankali ga duk alumma. Kowa yanzu kuka yake da hawaye saboda wahalar da ake sha.

Duk mu na gani, muna jin yadda iyaye da Ango ke kuka a kan wannan wahala da muka ɗora wa kanmu. Kawai don zuciyar yaranmu ta yi da]i, komai suke so, ba duba sai mu amince. Uwa ta ta da wa uban yara hankali ya fita ya nemo.

Saboda kada a a yi mata dariya ko a yi wa ‘yarta a cikin mutane, a ce sun gaza. Shi kuma haka zai shiga fafutuka ya yi wa asusunsa kaf! A taru bayan biki a tsuguna. Ko da rana ɗaya bai kawo abinci ba na tabbata uwa ita ce za ta fara ɗaga masa hankali, ya bar su da yunwa. Ta manta irin ta’asar da suka yi wa ajiyarsu.
 
Babban abu  ma fi mamaki idan ba a kama gurin biki ba, sai fa a fasa auren kawai. Kar uwa da ‘yarta su ji kunya. An sha ɗaga biki ko a fasa ma kwata-kwata saboda ango ba shi da shi, ko iyayen amarya ba su da shi. Ya ilahil alamina wannan ƙarya da muka ɗora wa kanmu har ina?

Muddin ba za mu gyara ba, mu fita sabgar yara mu koma mu yi komai cikin kulawa, yadda ya kamata. To muna shirin ajiye yaranmu mata a gaba. Su ma daga mazan da nasu. An gama baza ƙarya da kuri a majalisa. Ranar biki na sai na yi kaza, sai na yi kaza, sai an kawo min kaza. Duk irin waɗannan su ma suna daɗa lalata aure. Ba ka da gashin wancan, ka daure kar ka ce sai ka yi kitson wance. Don kowacce ƙwarya da abokin burminta.
Daga fannin maza da matan duk ƙarya ce tsababa, shi ya sa aure ke lilo. 

Kwanaki aure ya mutu a kan siyan bakin amarya. An fasa aure da yawa saboda Ango bai da kuɗin da zai ba wa amarya ta yi walima (party) ko ta kama guri. An sha aron lefe ana dawowa, a amshe bayan aure. An sha haɗa baki da angwaye a zo a sace lefe. Duk me ya jawo? Ƙarya ce kawai da son a sani. Don Allah wa gari ya waya?

Iyaye sun fi kowa laifi domin da ba su biye wa ruɗin duniya ba da tuni an manta da wannan kama guri, da sauransu. Mu kula dai mu sai wa yaranmu daraja, mu duba irin ɗaruruwan kuɗin da mu ke bayarwa kawai taro na wuni ɗaya.

Wannan baƙar rayuwa da muka ɗorawa kanmu take ta wahalar da mu, ya kamata a samu mafita a rage wasu abubuwan don mu samu daidaiton al’amurra. Yara a daɗa gaya musu rayuwa ba ɗaya ba ce. Shi aure fa albarka kawai ake nema da zaman lafiya, ba a buƙatar tsaurarawa don Allah. Iyaye da yara da mazan ma kansu a yi karatun nutsuwa.

Don ALLAH ina iyaye suke da suka bari wai namiji na aron kayan lefe? Aure idan ba ka da shi, ba a ce dole ka yi ba. Sai ka jira lokacin da ya dace. Ba ka ɗora wa kai ƙarya ba. Sanda aka zo karɓa, ido ya raina fata. Daga nan aure ya lalace, don amarya ba za ta yarda ba rigima ce za a yi ta, daga ƙarshe a rabu. Wasu kuma turawa suke yi a sace kayan lefen yadda ba za a zarge su ba. Duk irin wannan sakacin na iyaye ne gaskiya. Da sun nuna wa yaro amfanin neman na kai, da nuna masa ya yi abin da zai iya, na tabbata wani abin ba zai faru ba. To son yara yakan sa mu iyaye mu manta da duk wani abu mara daɗi da zai zo wanda sai ta faru a zo ana da an sani.

Amaren zamani: Su ne yanzu suke damalmala komai. Idan suka ga wasu masu halin sun yi abu, su ma sai su ce sai sun yi. Ya ilahi, ina ake haka ne? Dai-dai ruwa, dai-dai ƙurji. Duk rayuwa tana da lokacinta. Kar ki ɗaga wa kanki hankali, ki ɗaga wa wani. Ki yi yadda ƙarfinki ya ke, ba ki hango abinda zai rusa mi ki farin ciki ba. Don kowa da ku ka gani da abinda Allah ya ba shi a rayuwa, mu zamo masu gode wa Allah.

Don Allah iyaye mu taru mu gyara, mu bar wannan abubuwa da suka zamo mana masifa.

Kama wajen biki: A kama guri kusan miliyan ɗaya a lokaci ɗaya. Banda abinci, ruwa, da sauransu. Idan ka sa wannan kuɗin, zai iya saya maka ƙaramin gida, kuma za ka iya jari da sana’a. To a yi haƙuri, a yi abinda zai jawo alheri ba biyan bashi ba.

A gabana an yi rigma da amarya da iyayenta. Wallahi tace idan ba a yi mata gado biyu ba, to a fasa kai ta. Juyin Duniya ta ce, ita fa aure ta fasa. Don ta gaya wa ƙawayenta biyu za a mata. Shi ma angon ta faɗi ma sa, kuma yanzu su ga ba haka ba dariya za a yi mata.

Na yi mamaki da na ga iyayen suna lallaɓa ta. Idan sun samu za su yi mata. Ta dai yarda a ɗaura auren, amma fir ta ƙi. To ina amfanin wannan ɗan da ka haifa, ba ka isa da shi ba.

Wata kuma a kan kama gun biki ta gudu, don iyayenta sun gaza, shi ma Ango ya ce babu. Da ta ji kunya an yi bikinta a gida, gara ta gudu.

Matsaloli fa da yawa idan ba mu yunƙura mun gyara ba, to wallahi iyaye muna ruwa. Allah sa mu dace, Ya shirya ma na zuri’armu. Amin.

Wassallam, mu tara sati na gaba cikin jaridarmu mai albarka ta Blueprint Manhaja.