
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Jami’an Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati EFCC, sun yi nasarar kama tsohon Ministan Wutar lantarki, Saleh Mamman bayan tsawon lokaci yana ɓuya.
Hakan na zuwa ne bayan da kotu ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru 75 a gidan yari sakamakon samun sa da hannu a laifukan da suka shafi badaƙalar kuɗaɗe.
Rahotanni sun bayyana cewa jami’an EFCC sun cafke Mamman ne a unguwar Rigasa da ke jihar Kaduna da misalin ƙarfe 3:30 na yammacin ranar Talata.
A cewar masu bincike, an sha wahala wajen kama tsohon ministan saboda yawan sauye-sauyen layukan waya da lambobin waya da gidaje akai-akai.
Haka kuma, EFCC ta kama wasu mutane guda biyu da suka yi ta taimaka masa yayin da yake ɓuyar na tsawon lokacin da aka yi ana neman sa.
Shugaban hukumar, Ola Olukoyede ya sanar da kama Mamman ne yayin wata hira da manema labarai a Abuja, inda ya bayyana hakan a matsayin gagarumar nasara a ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya na yaƙi da rashawa akan waɗanda suke sauya akalar dukiyar ƙasa.
