Ban shiga ADC don zama mataimakin shugaban ƙasa ba, inji Amaechi kan zaɓen 2027

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon gwamnan jihar Ribas, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa ya shiga takarar shugaban ƙasa ne a jam’iyyar ADC a zaben 2027, domin ya cancanci sauke nauyin abin da Nijeriya ke buƙata wajen jagoranci, yana mai cewa ba matsayin mataimakin shugaban ƙasa yake nema ba.

Amaechi ya faɗi haka ne a Abuja a wata hira ta gudanar talabijin tare da Mohammed Hayatu-Deen da tsohon Maitaimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar da jaridar NewsPointNigeria ta ɗauko.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan takarar shugaban ƙasar na zaɓen 2027 a ADC ke shirin halartar tantancewa daga kwamitin tantance ‘yan takara na jam’iyyar da za a yi a ranar Laraba.

Amaechin ya kuma yi watsa da raɗe-raɗin cewa ana tattaunawa akan shirin yin sulhun tsayar da ɗan takara ɗaya da zai wakilci jam’iyyar a zaɓen shugaban ƙasa.

Tsohon ministan sufurin ya ƙara da cewa, ba shi da burin janye wa kowane ɗan takara da nufin karɓar muƙamin mataimakin shugaban ƙasa a ƙarƙashin haɗakar ‘yan siyasar.

A cewarsa, bai taɓa tsaya wa takarar shugaban kasa ba, don haka yana ganin hakan zai ba shi damar gabatar da kansa a matsayin sabon zaɓin al’ummar Nijeriya.

Saidai duk da wannan iƙirari, Amaechi ya yaba wa Atiku da kuma tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP, Peter Obi, yana mai cewa dukkansu za su iya mulkin Nijeriya fiye da Shugaba Bola Tinubu mai ci a yanzu.

By Babaji