Sarki Sanusi abokin ƙwarai ne, inji Jonathan yayin da suka yi kiciɓis a taron Gowon

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Ebele Jonathan, ya janyo cece-kuce a ranar Talata yayin da ya kira Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi na II da “abokina na ƙwarai” a wajen wani taron al’umma.

Jonathan ya yi wannan furuci ne a lokacin ƙaddamar da littafin ‘My Life of Duty and Allegiance’ wanda tsohon shugaban mulkin soji, Yakubu Gowon ya wallafa, ranar Talata.

Kalaman tuni suka sanya jama’ar wajen cikin nishaɗi, lamarin da ya sa aka dakatar da tsohon shugaban wanda ya jagoranci taron daga cigaba da jawabin karɓar baƙi.

Jonathan da Sanusi suna da daɗaɗɗen tarihin siyasa tun lokacin da Sarkin yake gwamna a Babban Bankin Nijeriya, CBN.

Alaƙarsu ta yi tsami ne a lokacin da zarge-zarge suka shiga tsakanin mutanen biyu, waɗanda suka haddasa cece-kuce a matakin ƙasa a wancan lokacin.

A ranar 13 ga watan Fabarairun 2014 ne a lokacin da Sanusi ya je gaban kwamitin kuɗi na Majalisar Dattawa, ya zargi Babban Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPC) da rashin shigar da Dala biliyan 20 acikin asusun ƙasa.

Wannan zargi ya haddasa cece-kucen siyasa a faɗin Nijeriya, inda wasu ke ganin hakan a matsayin dalilin haddasa tsamin dangantaka tsakanin Jonathan da gwamnan na CBN a lokacin.

Watanni bayan dakatar da shi daga jagorancin CBN, Sanusi ya zama sarkin Kano jim-kaɗan bayan rasuwar marigayi Sarki Ado Bayero a 2014.

By Babaji