Daga AISHA ASAS
A ranar Juma’ar da ta gabata, 29 ga watan Oktoba, Allah Ya yi wa shahararren marubucin littattafai kuma ɗaya daga cikin waɗanda su ka fara wasan kwaikwayo a arewacin Nijeriya, wato Alhaji Umaru Ɗanjuma Katsina, wanda aka fi sani da Kasagi rasuwa.
Marigayi Umaru Ɗanjuma Katsina ya yi fice ta fannin wasannin kwaikwayo kamar su ‘Magana Jari ce’, ‘Ruwan Bagaja’, ‘Kasagi’, ‘Ya’yan Zamani’ da sauransu. Sannan ya kasance ɗaya daga cikin marubutan da littafansu suka yi fice duniya ta san su. Wasu daga cikin littafan nasa sun haɗa da ‘Kulɓa na ɓarna’, ‘Ai Ga Irinta Nan’ da dai sauran su.
Wasu daga cikin mahallarta taron bikin Bajekolin Littafai da al’adun Hausa na duniya HIBAF, wanda ya gudana a Kaduna makon jiya, sun tabbatar da halartar taron nasa, har ma ya yi bayanai masu yawa kan kula da tarihin Hausawa da al’adunsu. An kuma karrama shi a wajen taron.
An haifi Alhaji Umaru Ɗanjuma Katsina a shekarar 1950 a unguwar Ƙofar Soro dake cikin Jihar Katsina, ya yi makarantar firamare a Giɗaɗo Primary School daga shekarar 1960 zuwa 1972, daga nan sai ya shiga makarantar Sakandaren gwamnati dake nan Katsina daga shekarar 1972 zuwa 1975.
Bayan ya kammala karatun sakandare, ya sami damar shiga wata Makarantar gaba da sakandare dake garin Landan a Ƙasar Burtaniya mai suna ‘Film and Television Training School’ inda ya ƙara gogewa a kan shirya wasannin kwaikwayo da shirye-shiryen gidan talabijin. Kusan duk wani karatu da Marubucin ya yi ya fi maida hankali kan waɗanda suka shafi rubutu da kuma wasan kwaikwayo.
Marubucin ya rasu ne a wani asibiti a Katsina, bayan gajeruwar jinya. Allah ya gafarta masa tare da sauran marubutan da suka riga mu gidan gaskiya.
