Abin da ya hana Gwamnati ayyana ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda – Ministan Tsaro

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ba haka kawai gabagaɗi ake fitowa a ayyana cewa ‘yan bindiga su ma ‘yan ta’adda ne ba.

Ministan Harkokin Tsaro, Bashir Magashi ne ya bayyana haka, tare da cewa, akwai matakan da ake bi, kuma ko an bi su ɗin, to sai an tabbatar da kammaluwarsu sannan za a ayyana cewa ‘yan bindiga ma ‘yan ta’adda ne.

Magashi ya yi wannan maganar ne a lokacin da ya kai ziyarar gani da ido don ganin irin ci gaban da ake samu a filin dagar yaƙi da Boko Haram a Maiduguri da ke Jihar Barno.

Ministan ya samu rakiyar Babban Hafsan Tsaron Ƙasa, Lucky Iraboh da sauran manyan hafsoshin ƙasa, ruwa da na sama.

Ya kuma gana da manyan kwamandojin yaƙi na Arewa maso Gabas, wato ‘Threater Commanders’, tare da nuna gamsuwa da irin ƙoƙarinsu da nasarorin da ake kan samu a yanzu.

Magashi ya yi wannan bayani ne biyo bayan tambayoyin da manema labarai su ka yi masa a Maiduguri, dangane da tsaikon da ake samu wajen ƙin kiran ‘yan bindiga da suna ‘yan ta’adda da Gwamnatin Tarayya ta ƙi yi.