Yadda wani ƙasurgumin ɗan bindiga ke neman tallafa wa mabiyansa a TikTok da kuɗi

Spread the love

Daga SANI HAMAD GIWA a Abuja

Wani abu mai kama da almara kuma abin haushi, inda wani ƙasurgumin ɗan ta’adda ya fito ƙarara a shafinsa na TikTok domin tallafa wa mabiyansa a shafin da kuɗi.

An saka bidiyon ne kai tsaye a shafin ɗ, wato Tiwita.

A yayin zaman, wanda tun daga lokacin ya fara yaɗuwa, an ga mabiyansa da dama suna raba lambobin asusunsu a sashin sharhi.

Hakan ya haifar da fushi, inda da yawa suka yi kira ga hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da sauran jami’an tsaro da su bi diddigin su tare da kama mutumin.

@reɓi_ofthehills, Comr. Isah Muhammed ya ce: “Jami’an tsaro ba za su iya gano shi ba saboda ba ya riƙe da allunan “kawo ƙarshen rashin shugabanci nagari”.

@solbabyz: “Gaskiya mutanen nan suna iya amfani da wayoyin hannu cikin kwanciyar hankali hauka ne ta yaya gwamnatin Nijeriya ba za ta iya samun fasahar gano su ba ko da wayoyin ba su da sim card?”

@Nairaeɗchanger: “Yana amfani da tsarin banki da sadarwa da kuma shafukan sada zumunta, gwamnati ta rufe ido. Duk wanda ya kira wannan gwamnati da ce wa ba ta da hannu, to wannan wawa ne gaba ɗaya.”

@Ezeifeka_Obinna: “Ban san dalilin da ya sa sojoji ke da jirage marasa matuƙa ba, kama mutanen banzan nan abu ne mai sauƙi.”

@moright20: “Ya kamata gwamnati ta hana TikTok.”

@ontophilll_: “Me ya sa DSS ba za ta iya amfani da bayanan mai aikawa daga banki da bin diddigin su ba.”

@pdauda: “Koyaushe ‘yan fashinmu suna sanye da kayan aikin GI da cikakkun kayan haɗi da makamai. Irin camo da sojoji za su sa matasa su rika birgima a cikin kwalta don sanyawa shi ne abin da ‘yan ta’adda da ‘yan fashi ke nunawa. Kuma CDS ko COAS ba sa husuma da tada hankali.

@abn_charles: “Ina mamaki ooo! Ina shakka @PoliceNG na iya ganin bidiyo irin wannan ko kuma sun shagaltu da zanga-zangar da mutane marasa lahani.”

A halin da ake ciki, kakakin rundunar ‘yan sandan Nijeriya, Muyiwa Adejobi, ya mayar da martani yana mai cewa ‘yan sanda ba za su iya kama duk masu aikata laifuka a lokaci ɗaya ba.

A wani saƙon da ya fitar ta hanyar ɗ, Adejobi ya shaidawa ‘yan Nijeriya cewa, maimakon su yi tsammanin za a kama dukkan ‘yan ta’adda a lokaci ɗaya, ya kamata su yaba da kama su da aka yi, domin suna iya baƙin ƙoƙarinsu.

Yana mayar da martani ne ga wasu hotuna guda uku da wani mai amfani da ɗ ya wallafa wanda ke nuna wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne suna bajekolin takardun Naira da ake zargin suna karɓa a matsayin kuɗin fansa ne.

Rundunar ta PRO ta ce, “Ba za mu iya kama dukkan masu laifin a lokaci ɗaya ba. Aƙalla, ku yaba mana da waɗanda muka kama. Muna kama su a kullum, da yawa.

“Rundunar soji da ‘yan sanda suna bakin ƙoƙarinsu. Yakamata a gani, a lura da ƙoƙarin jami’an tsaro, a kuma yaba da su. Ya kamata mu duba yadda za mu yi ƙoƙarin haɗin gwiwa da kuma sa hannun ɗaiɗaikun mutane wajen magance matsalar rashin tsaro da sauran munanan ɗabi’u a Nijeriya.”

By ukarofi