Yadda ya kamata gasar Olympics ta kasance

Sharhi daga LUBABATU LEI

Jama’a, shin me za ku ce game da ma’anar gudanar da gasar wasanni ta Olympics?

Yin takara don neman cin lambobi ne? Babu shakka, wannan wani ɓangare ne na gasar, amma ba shi ke nan ba.

‘Yan kwanaki suka rage za a kawo ƙarshen gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi da ke gudana a nan birnin Beijing. A cikin kwanakin da suka gabata, yadda ‘yan wasan daga ƙasa da ƙasa suka ƙoƙarta matuƙa, don cimma ƙarin nasarori a yayin gasar ya burge mu ainun, sai dai baya ga haka, yadda ‘yan wasan suke cuɗanya da juna bayan gasar ya fi sosa mana rai.

Kwanan baya, ’yar wasan ƙasar Sin Xu Mengtao ta zama zakara da maki 108.61, a wasan tseren ƙanƙara da ake sarrafa jiki a iska na Freestyle Skiing na gasar. Nan da nan, ‘yar wasan ƙasar Amurka Ashley Caldwell ta rungume ta, har hawaye ya zubo mata saboda murna. Ta ce, yadda Xu Mengtao ta yi iyakacin ƙoƙari a gasar ta burge ta, kuma ya sa tana girmama ta. Ta yi murna da yadda Xu mengtao ta cimma mafarkinta a asarta ta mahaifa.

A gasar wasan Curling, ‘yan wasan ƙasar Amurka Vicky Persinger da Chris Plys, sun yi nasara a kan ‘yan wasan ƙasar Sin Ling Zhi da Fan Suyuan. Bayan da gasar ta ƙare, ‘yan wasan ƙasar Sin sun miƙa wa abokan takararsu ‘yan tsarabobi, wato bajoji masu siffar Bing Dwen Dwen, ‘yar tsanar gasar a wannan karo, matakin da ya burge ‘yan wasan Amurka, har suka bayyana cewa “so cool” wato dai hakan ya burge su, kuma sun saka hotonsu a shafinsu na sada zumunta. Kafar NHK ta ƙasar Japan ma ta ce, gasar ta kusantar da ‘yan wasan ƙasashen biyu da juna.

Bayan gasar tseren ƙanƙara ta gajeren zango, ta yada ƙanin wani ta mita 3000 ajin mata, ‘yan wasan ƙungiyoyin ƙasashen Netherlands, da Koriya ta Kudu, da ƙasar Sin, da suka ci lambobin zinari da azurfa da tagulla, sun haɗu sun ɗauki kansu hotuna na selfie, cikin murna da farin ciki……

A gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing, an sha ganin irin zumuntar da ‘yan wasan suka ƙulla. Lallai, ‘yan wasan dake fafatawa a gasar abokan takara ne, sai dai kuma sun kasance aminan juna da ke neman ƙarin ci gaban ɗan Adam kafaɗa da kafaɗa.

Yadda aka gudanar da gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing bisa lokacin da aka tsaida, ya samar da wata gadar fahimtar juna a tsakanin ‘yan wasan ƙasashe daban-daban, tare da samar da damar ƙarfafa haɗin kan ‘yan Adam, kuma ‘yan wasan gasar sun shaida mana ruhin gasar, wato “Faster Higher Stronger da ma Together”. Wato ƙarin sauri, ɗagawa, ƙarfi da tafiya tare”.