Buɗaɗɗiyar wasiƙa zuwa ga Shugaban Hukumar Kwastom), Kanar Hamid Ali

Daga NAFI’U SALISU

Yin kyakkyawan bincike ta hanyar da ta dace da kuma gani da ido, su ne abubuwan da suke tabbatar da abinda yake wakana a cikin al’umma, ko sun yi ƙorafi ko ba su yi ba.

Tun bayan ɗarewar s’Shugaba Muhammadu Buhari kan ƙaragar mulkin ƙasar Nijeriya, an ga yadda jami’an hukumar hana fasa-ƙwauri (Kwastom) suka yawaita a manya da ƙananan titunan ƙasar. Abinda  a zahirance ke nuna manufar barbaza su a ko’ina shi ne, don su daƙile ayyukan fasa-ƙwauri na kayayyakin da Gwamnatin Nijeriya ƙarƙashin mulkin Muhammadu Buhari ta hana shigowa da su cikin ƙasar nan ko fita da su.

Abu na farko da kowa ya fi sanin an hana shigowa da shi, shinkafa ce.  Wacce aka yi dokar hana shigowarta bayan rufe iyakar ƙasa, da yunƙurin Gwamnati na samar da noman shinkafa a cikin ƙasa da zummar ciyar da ƙasa gaba da abinci. Ko shakka babu, idan da wannan manufar ne Gwamnati tayi haka, to wannan abu ne mai kyau, abu ne da idan ya tabbata al’ummar ƙasa za su yi farin ciki, sannan ƙasa za ta bunƙasa.

Bayan shinkafa da ita ce babbar abinda aka yi hanin ganin an shigo da ita, sai kuma makamai da sauran wasu kayayyaki. Kodayake, ita ɗin ma an ce akwai hanyar da aka yarda a shigo da ita (a wata majiyar kenan). To amma dai shigo da ita ta kan iyakokin ƙasa shi ne babban laifi. Akwai kayayyaki da dama da Gwamnati ta yarda a shigo da su ta hanyar da ta aminta, tare da haraji mai ƙarfi wanda ‘yan kasuwa suke biya da Gwamnati ta saka masu, kuma suna biyan wannan haraji ne ta hannun ita hukumar hana fasa-ƙwauri (Kwastom), shi ne abin da a ke kira da (Custom Duty). Duk wani kaya da ake shigowa da shi da aka biya masa wannan haraji, ana siyar da shi ne a fili a cikin dukkannin kasuwanninmu da ke faɗin Nijeriya. Kuma idan an biya ma sa wannan haraji, akan shigar da shi lungu da saƙo.

Misali; mu ɗauki kamar Garin Kano, wanda garin Kano gari ne da kowa ya sani cewa, garin kasuwanci ne. Kuma ƙarfin kasuwancin Kano ya shafi dukkan ƙarfin kasuwancin Nijeriya. A yayin da ƙarfin kasuwancin Kano ya durƙushe, to duk wani tasiri na kasuwanci a Nijeriya zai tavu magashiyyan, domin ita ce Cibiyar Kasuwanci (Center of Commerce ).

Sai dai a halin da ake ciki, an ɗauki lokaci a na yi wa wannan kasuwanci bi-ta-da-ƙulli a jihar Kano, wanda har ta kai wasu ‘yan kasuwa da su ke shiga Kano domin yin siyayyar kayayyaki sun haƙura da zuwa Kanon. Dalili kuwa shi ne, sun ce idan sun sawo kayan suna fuskantar matsaloli na jami’an hanya, kuma jami’an da suka fi uzzura musu a kan kayansu jami’an Kwastom ne. 

Sannan uwa-uba direbobin da suke ɗauko kayan zuwa garuruwa daban-daban, da suka haɗar da; Zariya, Kaduna, Abuja, Katsina, Zamfara, Sakkwato da sauransu. Idan Direbobi suka ɗauko kaya daga Kano, musamman idan kayan sun shafi kwali, atamfa ko wani abu da ya shafi a cikin leda ko buhu, sai jami’an kwastom sun tsare su sun karɓi kuɗi a wajensu, koda wannan kayan da suka ɗauko ba shi da alaƙa da jami’an hana fasa-ƙwaurin. To idan muka dubi wannan, me za a kira shi a zahirance da baɗinance? Kun ga kenan cin hanci ne suke karɓa, wanda kuma karɓar cin hanci a dokar ƙasa babban laifi ne da ya saɓa wa shari’a. Domin duk wani kaya da za a shigo da shi cikin ƙasar Nijeriya, har a zo a kasa wannan kayan a kasuwa, to dole sai ka samu an biya mishi (Custom Duty), idan wanda ya shafi kwastom ɗin ne. To kayan da bai shafe su ba kuma mene ne haɗinsu da shi? 

Idan Direba ya ɗauko leda, ko kayan robobi daga Kano zai tafi Abuja ko Kaduna, ko ya ɗauko kwalayen da a cikinsu kayan wasan yara ne zai kai Kaduna ko Abuja, mene ne dalilin da zai sa jami’in kwastom ya tsare shi ya ce lallai sai ya karɓi kuɗi a hannunsa? Wannan zalunci ne da kuma zubar da ƙimar ƙasa da wulaƙanta aikinsu.

Ni ɗin nan na shiga mota zuwa Kaduna, muna zuwa Daka-tsalle, jami’an kwastom suka tare mu sai da suka karɓi kuɗi a hannun direban motar da nake ciki, wai saboda ganin ya ɗauko kwalaye a motarsa. Kuma wallahi tallahi kayan hanga ne irin na rataye kayan yara idan an wanke ne, sai kuma kayan wasannin yara a cikin kwalayen, domin a gabana aka loda kayan a motar da na shigo. Allah Shi ne shaidata, kuma zan tsaya a gabanSa ranar ƙiyama. Amma wallahi tallahi sai da jami’an kwastom suka karɓi kuɗi a hannunsa, bayan ya faɗa musu abinda ke cikin kwalin, sun kuma zo sun duba sun gani da idonsu, domin akwai kwalayen da a yage suke ana ganin abinda ke ciki.

Bayan mun bar wajen, harwayau kuma mun zo Zariya, idan an wuto Masallacin matafiya na Marigayi Umaru Musa ‘Yar’aduwa, a nan ma akwai shingen bincike na jami’an kwastam, wanda a zahiri ne kawai yake shigen bincike. Amma a baɗini, shigen cutar direbobi da ‘yan kasuwa ne na karɓar kuɗaɗe a hannunsu. Shigen baƙin kasuwanci ne na karɓar cin hanci na tilas da jami’an kwastom suke yi. 

A lokacin da mu ka zo wannan wajen, sun tsaida mu, muka tsaya. Bayan mun tsaya, direbanmu ya faɗa musu abinda ya ɗauko, kuma suma sun gani, amma buɗar bakin ɗaya sai cewa ya yi direbanmu ya kawo dubu ɗaya. Da yake dare ne, haka direban ya ɗauki dubun ya ba shi (don kar ya ɓata mana lokaci). Can kuma sai ga wani dogo siriri ya zo shi ma wai sai ya karɓa. Kuma ya kafe a kan cewa shi dubu da ɗari biyar za a ba shi. Da naga abin ya zamo rainin wayo da zalunci, sai na sauka zan saka baki, amma sai shi jami’in kwastom ɗin ya nuna babu ruwana, wannan tsakaninsa da direba ne. Wallahi sai da Direban ya biya wannan kuɗin. Ka ga kenan ya ba su dubu biyu da ɗari biyar.

To a nan don Allah mu fahimci wani abu, idan direbobi za su riƙa ɗauko shinkafar waje da Gwamnati ta hana a shigo da ita, kun ga kenan kuɗi kawai za su raba wa jami’an hana fasa-ƙwauri (Kwastom) su bar su su wuce. Don haka kun ga za a iya shigowa da makamai bayan shinkafar, domin idan har jami’an tsaro da ke bisa hanya, wanda manufar tsayuwarsa a hanya shi ne ya kama kayan laifi, ko daƙile aikata laifi, to idan har zai karɓi kuɗi a hannun masu wucewa a hanyar, ta yaya zai daƙile wani mummunan aiki da ake aikatawa a cikin ƙasa? Babu! Wannan shi ne babban ƙalubalen da yake ƙara sa tsaro yana taɓarɓarewa. 

A zahirin gaskiya, ba wai jami’an kwastom kaɗai ba, duk wani jami’in da yake karvar kuɗi a hannun Direbobi ko ‘yan kasuwa bisa hanya, to shi a kansa babbar matsala ce a ƙasa. Domin shi a matsayinsa na wanda yake jami’in tsaro, wanda aikinsa shi ne ya kare rayuka da dukiyar al’umma, ta hanyar daƙile aikata munanan laifuka, amma a ce yana karɓar kuɗaɗe a hannun al’umma, to ta ya ya aikata laifi zai fasu? Maimakon haka ma sai dai aikata miyagun laifukan ya ƙaru.

Don haka ni Ina kira da jan hankali ga shi shugaban hukumar kwastom ya yi duba a kan ire-iren waɗannan matsaloli, waɗanda su ne suke taka rawa wajen samar da rashin nasara a yayin gudanar da aikinsa na tabbatar da an samu nasara a aikin hana fasa ƙwauri. 

Sannan, matuƙar dai ana son a samu nasara a fannin daƙile shigo da miyagun kayayyaki, makamai da sauransu, to ya zama tilas hukumar kwastom, ƙarƙashin jagorancin mai girma Kanal Hamid Ali (Mai ritaya) ta qara sa ido sosai a kan jami’anta na kwastom, ta tabbatar da sun tsaya a kan aikinsu, sun daina karvar kuɗaɗe a wajen direbobi don kawai direba ya ɗauko atamfa daga kasuwar Kano, ko kwalayen da a cikinsu ba kayan laifi ba ne da aka yi hani a ɗauko, ko a shiga da su wata jiha ba. Idan kuma  ba haka ba, to wannan ya zama zalunci ga su direbobi masu dakon kaya, da ‘yan kasuwa da ma su kansu masu zuwa sayen kayan. Kuma wannan lalata harkar kasuwanci ne, wanda muke gani ana yi a halin yanzu, wanda su ‘yan kasuwar suke kokawa,  haka ma waɗanda suke zuwa sayen kayan suna kokawa, duk a dalilin takurawa da cin zalin da jami’an kwastom suke yi masu.

Kuma magana ta gaskiya, karɓar kuɗaɗen da jami’an kwastom suke yi a hannun direbobi, abu ne da yake kawo matsala a fannin tsaro. Domin matuƙar direba ya san cewa kuɗi kawai jami’in kwastom zai karɓa a gare shi yayin da ya zo shigen bincikensa, to kowanne irin kayan laifi aka ba shi zai ɗauka, kuma zai kai su duk inda ake so ya kai. Ka ga kenan hatta makamai idan an ba direba zai ɗauka ba tare da fargaba ba, domin ya sa daga dubu ɗaya zuwa dubu biyu za ta raba shi da jami’in hana fasa-ƙwauri.

Tabbas karɓar kuɗi a hannun direbobi da jami’an tsaro suke yi (ba sai jami’in kwastom ba), babbar matsala ce mai kawo naƙasu ga sha’anin al’amurran tsaro a ƙasar nan. Kuma su manya ya kamata su fahimci wannan, domin ko da su direbobin a cikinsu akwai waɗanda suke tsoron Ubangiji, kuma ba sa dakon kayan laifi, to fa wasu saboda wannan takurawar da jami’an kwastom suke yi musu ta karɓar kuɗi a hannunsu, hakan zai iya sakawa su ɗauko kayan laifin da aka yi hanin shigo da su cikin ƙasa, ko kai su wasu jihohi. Sai su ɗauko su kai su duk inda ake so su kai, saboda sun sani cewa kuɗi ne zai raba su da jami’an ba za a bincike su ba.

Ya kamata mu sani cewa, matuƙar dai jami’an kwastom za su cigaba da karɓar kuɗi a hannun direbobi, to maganar kawo ƙarshen shigo da kayan laifi, ko raba su a wasu jihohi ma ba ta taso ba. Kamar yadda nake so a fahimta, idan fa wasu direbobin ba su ɗauki kayan laifi ba, to tabbas wasu za su ɗauka, dalili kuwa shi ne, sun san cewa kuɗi za su bayar a duk wani shingen bincike su wuce ba tare da an binciki me suka ɗauko ba. Haka duk wani jami’in tsaro ba ma sai jami’in kwastom ba, matuƙar dai jami’in tsaro zai ci gaba da karɓar cin hanci a gurin direbobi, to ba za a taɓa samun nasarar kawo ƙarshen matsalar tsaro ba.

Da wannan nake kira ga shugaban hukumar hana fasa ƙwauri, Kanal Hamid Ali (Mai ritaya), ya yi duk mai yiwuwa domin maganace wannan babbar matsalar. Matsala ce mai muni, wadda muninta ya fi duk yadda za a auna a sikeli. Matsala ce da idan har ba a magance ta ba, to hakan zai ci gaba da taimaka wa ‘yan ta’adda wajen safarar makamai daga wata ƙasa zuwa ƙasar nan, daga jiha zuwa wasu jihohin ƙasar nan. Don haka, a ɗauki mataki matuƙar ana son a kawo ƙarshen matsalar tsaro, da kuma daƙile yaɗuwar makamai a ko’ina. Sannan su kansu direbobi za su yi aikinsu a cikin kwanciyar hankali.

Nafi’u Salisu, Marubuci/Manazarci,
[email protected] da [email protected]