Namiji mai tsafta

Daga AISHA ASAS

A lokacin da mace ta zama ƙazama, za ka ji ana tsorata ta da cewar, ba za ta samu mijin aure ba. Amma duk ƙazantar namiji sai ka ji ana cewa, ya dai nemi kuɗi, ba zai rasa matar aure ba. Abin tambaya, shin su matan ba sa duba tsafta a cikin rukunan zaɓinsu ga aure? Ko ita mace ba ta buƙatar namiji mai tsafta wurin samun nutsuwa a zaman aure? Shafin iyali na wannan sati zai tattauna kan wannan matsala tare da jin ra’ayoyin wasu mata akan wannan maudu’i. Kasancewar mata na da mabanbantan ra’ayi kan muhimancin tsaftar namiji a zamantakewar aure. Wasu na ganin ba shi da wani tasiri a zaman aure, yayin da wasu ke ganin sa a matsayin babban ƙalubale a rayuwar aure. Wasu matan na ganin ba ta inda rashin tsaftar mijinsu zai zama matsala garesu, musamman idan yana ɗauke masu lalurorinsu. Idan kun shirya, mu ji daga bakin wasu daga cikin mata:

Ko auren namiji mai tsafta na da tasiri a zamantakewar aure?

Tsaftar ɗa namiji tana da babban tasiri a cikin zamantakewar aure. A na wa ra’ayin ma gara mace ta kasance marar tsafta da namiji ya kasance marar tsafta.

Dalilina na cewa hakan kuwa shine; Ita ‘ya mace tana jurewa tashin hankalin ɗa namiji. Ina nufin zai iya tanƙwarata idan ba ta yi tsafta ba, har ma ya kai ƙararta gidansu. Zai iya juya mata baya idan ba ta da tsafta, zai iya ƙaro aure a matsayin horo. Kuma cikin ikon Allah sai ta gyara ɗin. Amma namiji fa? Idan namiji bai da tsafta matarsa ta banu. Wallahi akwai wanda har ruwan wankan za ta kai masa ta roƙe shi Allah da Annabi ya je ya yi wankan, amma fir ya nuna mata ba zai yi ba, babu kuma wanda ya isa ya sanya shi ya yi ɗin.

Tsaftar ɗa namiji ta fi abubuwa masu yawa tasiri a zamantakewar aure. Mace za ta gyara gidanta, ta gyara gado, ta sa turaren wuta, tana jiran miji ya dawo. Yana dawo wa nan zai haye mata gado, ga warin hammata, ga warin rana. Daga nan sai ƙamshin ɗakin ya sauya zuwa wani abu kuma daban.
A yanzu mata sun gane, da su auri ƙazamin namiji mai kuɗi, gara su auri ɗa namiji mai tsafta talaka.

Daga bakin FATIMA IBRAHIM ƊANBORNO.

Za ki iya auren namiji ƙazami idan har sauran halayyarsa sun yi daidai da ra’ayinki?

Sosai kuwa, domin ai tsafta ado ce a cikin aure, kinga ko ba za ta iya zama silar aure ko barinsa ba. Ai gara a ce kina da miji ƙazami da a ce kina da mashayi, ko mai bugunki, ko wanda ke barinki da yunwa. A zamanin da mu ke ciki yanzu, idan dai zai cika ma ki cikinki, kuma ba bugu a zaman, to ya yi ta zama da ƙazantarsa. Zan iya saba wa da jin warin jikinsa, amma ba zan iya sabo da yunwa ko bugu ba.

Wani lokacin wasu matan na ba ni mamaki, ko da yake ba su san matsalolin aure ba, don da ba za su kawo tsafta ma a jerin zaɓin miji ba. Ai a da ne ake ta kan tsafta, amma yanzu ai sai dai ta nagari. Matsalar ci da sha kawai ta isa ta hana mace lura da yanayin mijinta, ma’ana, yana wanka ko yana wari.

Daga HALIMATU MUHAMMAD

Idan namiji na da kyakkyawan hali da kuma wadata, ko rashin tsafta na iya kawo cikas a zaman aurensa?

Ƙwarai da gaske. Ai kafin ma mu je ko ina a addininsa ma matsalarsa sai ta kawo masa cikas, ballantana a aure. Saboda an ce ‘Alnazafatu minal iman’.

Ai duk kyan halin mutum da nauyin aljihunsa, matuƙar bai da tsafta, to ya samu tasgaro, don ba ƙaramar mace marar ƙyanƙyami ce za ta iya jure zama da shi ba.

Don wani ƙazamin namijin duk iyayin mace ba ta iya canza shi, idan kuwa ta takura masa to fa ta ɗaura aure da fitina. Don da tai magana zai zaburo mata, shi a wurinsa ai shi ne mai gida, duk abin da zai yi daidai ne, babu wanda ya isa ya gyara masa. Ire-iren wannan suna haifar da tarin matsaloli a cikin gida.

Daga FATIMA USAINI EL- LADAN