Daga BELLO A. BABAJI
Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin ƙasa Ta’annati, EFCC ta tabbatar da kamawa tare da tsare tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello.
Kakakin hukumar, Dele Oyewale ya bayyana hakan a yayin hira da manema labarai a ranar Talata inda ya ce Yahaya Bello na amsa tambayoyi daga wasu jami’an bincike na EFCC.
Ya ce za kuma a gabatar da shi a gaban kotu bayan an kammala bincike akan sa.
A gefe guda kuma, a miƙa ƙarar ne ga Mai Shari’a Maryanne Anenih ta Babbar Kotun Abuja inda a nan ne aka maka tsohon gwamnan, wanda ake zarginsa da sauya akalar Naira biliyan 110 daga asusun jiharsa.
A ranar 14 ga watan Nuwamba ne aka zaɓi 27 ga wata, wato yau kenan, don gurfanar da shi a kotun.