Yahaya Augie ya yaba wa gwamnan Kebbi kan zaɓen Ibrahim Augie

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Shugaban ƙaramar hukumar Augie Honarabul Yahaya Muhammed Augie ya yaba wa Gwamna Nasir bisa ga zaƙulo Alhaji Ibrahim Augie a matsayin sabon mataimakin gwamnan jihar Kebbi.
Ya bayyana haka ne a garin Augie mahaifar sabon ɗan takarar mataimakin gwamnan.
Ya ce ba shakka gwamnan ya ɗauko mutum mai dattako da kuma sanin makamar aiki wanda ya goge.

Ya bayyana cewa wannan ya nuna irin soyayya da mutuntawar sa da mutanen masarautar Argungu saboda wannan ba ta tsaya ga Ibrahim Augie ko ƙaramar hukumar Augie kaɗai ba ce.
Ya kuma bayar da tabbacin goyon bayan sa tare da yin kira ga al’umma da su ba shi cikakken goyon baya don ganin an sami nasarori musamman ganin babban zaɓen shekarar 2027 yana ƙaratowa.

By ukarofi

Leave a Reply