
Daga BELLO A. BABAJI
Tsohon gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, ya bar ofishin hukumar hana yi wa tattalin arzikin ƙasa ta’annati (EFCC) kafin a gudanar da bincike akan sa.
A safiyar ranar Laraba ne kakakinsa, Ohiare Michael ya ce tsohon gwamnan ya amsa gayyatar da EFCC ta yi masa.
Yayin da ya ke bayani game da halin da ake ciki, Michael ya ce, hukumar ba ta gudanar da bincike akan Yahaya Bello ba inda aka samun wasu jami’ai da suka ce masa “zai iya tafiya.”
A safiyar Laraba ne Kakakin nasa ya ruwaito cewa, Yahaya Bello ya amsa gayyatar da hukumar ta yi masa saboda girmamawa da ya ke yi wa dokar ƙasa, ya na mai cewa an samu jinkirin hakan ne don a tabbatar da bin hanyoyin da doka ta samar a hukumance.
Ya kuma ce, kawo yanzu ba su san mai ake nufi da ce masa ya tafi ba da aka yi a ofishin hukumar da kuma dalilan yin hakan.
