
Daga BELLO A. BABAJI
Ma’aikatar Ilimi ta ƙaryata jita-jitar da ke yawo na cewa ƴan ƙasa da shekaru 18 ba za su rubuta jarrabawar WAEC da NECO ba.
Ƙaramin Ministan Ma’aikatar, Yusuf Sununu ya faɗi hakan a Abuja yayin ganawa da manema labarai a bikin ranar Ilimi ta ƙasa-da-ƙasa (ILD).
Ya ce, rashin fahimtar saƙon da ma’aikatar ta fitar a watan Agusta ya kai ga haka inda a baya Ministan Ma’aikatar, Tahir Mamman ya tattauna game da batun tsarin ilimi da shekarun da ya dace yaro ya shiga makarantar gaba da sekandire.
Hakan na zuwa ne bayan da gidan talabijin na ‘channels’ ya yi hira da Minista Tahir Mamman inda ya ke cewa ba za a sake barin ɗaliban da ba su kai wani mataki na shekaru ba su rubuta jarrabawar WAEC ko NECO.
A cikin jawabinsa bai ƙayyade shekarun ba, illa iyaka, ya yi la’akari ne da tsarin ɗaukar ilimi a Nijeriya na 6.3.3.4.
