‘Yan bindiga sun ƙi daina ta’addanci ne saboda gwamnati ta ƙi ba su wadatattun kuɗi – Dr. Gumi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Sanannen malamin addinin Musuluncin nan da ke Kaduna, Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya bayyana cewa ‘yan bindiga sun ki su daina ta’addanci ne saboda gwamnati ta ki ba su gonaki da kuma “wadatattun kuɗaɗe.”

Sheikh Gumi ya ce zaman sasanci da aka yi a baya don kawo zaman lafiya tsakanin ‘yan bindiga da al’ummar gari ya ciri tura ne saboda rashin biyan su diyya da “gonaki ko shanu ko kuma manyan kuɗaɗen da za su bar aikata wannan ta’asa.”

Gumi ya bayyana hakan ne a cikin wani karatu nasa da aka sanya kaitsaye a shafin sa na Facebook ranar Talata.

Ya ƙara da cewa wasu lokuta gwamnati “kawai sai ta ba su (‘yan bindiga) miliyan ɗaya ko biyu su samu na makamai ba tare da duban yadda suke rayuwa ba.”

Idan ba a manta ba Sheikh Gumi ya tava kwatanta ‘yan bindiga da tsagerun Neja Delta, inda ya nuna cewa duk tafiyar su ɗaya. Ya ce kuma gwamnati ta ƙirƙiro da hukuma ko ma’aikata a tarayyar Nijeriya da za ta shawo kan matsalar kashe-kashen Fulani makiyaya da ake yawan yi, musamman a kudancin ƙasar.

Haka kuma, idan ba a manta kwanakin baya an ga Sheikh Dr. Gumi yana kutsawa cikin dazukan da suka yi ƙaurin suna da mafakar ‘yan ta’adda, ciki har da dazukan Birnin Gwari, Giwa, Chikun da ke a Jihar Kaduna da kuma dazukan Jihar Neja, Sakkwato da Zamfara domin yin sulhu da ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane, inda ya yi zama da manyan-manyan kwamandojin daji irinsu Dogo Gide (da aka kashe kwanan nan a Kaduna) da Bello Turji da Ɓaleri da Ɗan-Small da sauran su.

Amma gwamnoni irin su Aminu Bello Masari na Jihar Katsina da Gwamna Nasiru El-Rufai na Jihar Kaduna sun barranta da ra’ayin Dr. Gumi na yin sulhu da ‘yan bindigar, inda Aminu Bello Masari ya fito fili ya alaƙanta yawancin Fulani cikin kashe-kashe da garkuwa da mutanen da ake fama da su, ya ce bai kamata a yi sulhu da su ko a raga mu su ba.