‘Yan bindiga sun kashe mutane 13, sun yi awon gaba da masu ɗaurin aure a Kaduna

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Ibtila’in ayyukan ‘yan bindiga ya samu al’ummar ƙauyen Kahir da ke ƙaramar Hukumar Kagarko a jihar Kaduna, inda wasu ‘yan bindiga a ranar Lahadi suka dirar wa ƙauyen ana bikin ɗaurin aure tare da kashe mutane 13 da aka gayyata da sace wasu da dama.

Mazauna ƙauyen sun ce an kai harin ne da misalin ƙarfe 11:47 na rana wanda ya haifar da tsoro a faɗin ƙauyukan da ke ƙaramar hukumar tare da tilasta wa wasu da dama guduwa su bar gidajensu.

Maharan sun zo ne da yawansu tare da manyan makamai inda suka kutsa wajen taron tare da buɗe wa baƙin da aka gayyata wuta.

“Tuni aka kai da yawan mutane babban asibitin Kagarko a yayin da waɗanda suke cikin mawuyacin hali aka kai su babban wani babban asibiti a Kaduna” a cewar wani mazaunin ƙauyen, Shehu Bala, kamar yadda ya shaida wa manema labarai a Kaduna.

Ya ce ƙara da cewa ba a san adadin mutanen da aka yi garkuwa da su saboda tashin hankalin da ake ciki saboda akwai mutane da dama da ba a san inda suka shiga ba.

Bala ya ce ‘yan bindigar sun ci karensu ba babbaka har na awa ɗaya inda suka fasa shaguna suka sace kayan abinci da magunguna.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Kaduna, Mansir Hassan, ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce nan gaba kaɗan za su fitar da cikakken rahoto kan lamarin bayan gudanar da binciken farko.

Haka kuma mazauna ƙauyen sun ce mataimakiyar gwamnan Kaduna, Hadiza Balarabe, ta jagoranci tawagar manyan jami’an gwamnati waɗanda suka kai ziyara ga waɗanda suka jikkata da ake duba su a asibiti.

Irin waɗannan hare-hare sun zama ruwan dare a Kudancin Kaduna da wasu sassa na jihar. ƙaramar hukumar Kagarko na cikin ƙananan hukumomin da ‘yan bindiga suka sa a gaba da garkuwa da mutane saboda yanayin wurin.

Kagarko ta kasance wata mahaɗa ce tsakanin jihar Kaduna da Filato da babbar birnin tarayya Abuja.

Kusancinta da babbar hanyar Abuja-Kaduna ya sa ta zama wani wuri na musamman ga masu garkuwa da mutane da suke kai farmaki tare da guduwa cikin ƙasurgumin dajin da ke iyaka da babban birnin tarayyar.

By ukarofi