‘Yan bindiga sun sace ɗaliban firame a Nasarawa

Daga BASHIR ISAH

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai hari tare da yin awon gaba da ɗaliban da ba a tantance yawansu ba a wata makarantar firamare da ke ƙauyen Alwaza cikin Ƙaramar Hukumar Doma, Jihar Nasarawa.

Jaridar Intelrigion ta rawaito maharan sun yi wa makarantar kwanton ɓauna ne a lokacin da yaran ke ƙoƙarin haɗuwa da safiyar Juma’a.

Ya zuwa haɗa wannan rahoto, ba a kai ga sanin su wane ne maharan da kuma adadin yaran da suka sace ɗin ba.

Da aka nemi jin ta bakinsa kan lamarin, mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, DSP Rahman Nansel, ya tabbatar da faruwar hakan.

A cewar rundunar ‘yan sandan jihar, an haɗa tawagar jami’an tsaro ta musamman da ta ƙunshi ‘yan sanda da sojoji da bijilanti domin bin sawun maharan.