Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
‘Yan bindiga a jihar Zamfara sun yi garkuwa da aƙalla mutane 46 yayin wani hari da su ka kai kan al’ummar garin Gana da ke jihar.
Rfi ta rawaito cewa masu tayar da hankali na zuwa a dai dai lokacin da wasu majiyoyi ke cewa ɗan bindigar daji Dogo Giɗe ya sanyawa wasu garuruwa 23 a ƙaramar hukumar Tsafe duk cikin jihar ta Zamfara harajin naira miliyan 100 bisa sharaɗin kai musu hari matuƙar suka gaza haɗa adadin kuɗin da ya nema.
Sai dai kuma a zantawar da sashen Hausa na RFI ya yi da mazauna yankin sun ce babu batu mai kama da wannan barazana.
Kafofin yaɗa labarai na ciki da wajen Nijeriya sun ruwaito yadda gomman ‘yan bindigar suka farmaki garin Gana a jihar Zamfara cikin ranakun ƙarshen mako tare da buɗe wuta kan jama’a wanda ya kai ga ƙone tarin gidajen da wuraren sana’ar jama’a gabanin sace tarin mutane ciki har da mata da ƙananan yara.
Wannan hari na zuwa bayan makamancinsa a watan da ya gabata, wanda shi ma ya kai ga sace tarin mutane, a wani yanayi da ake ganin dawowar makamantan hare-haren da kuwa garkuwa da mutane.
