Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnatin Jihar Katsina ta raba babura 50 ga jami’an kula da ingancin ilimi da sa ido kan makarantu a faɗin jihar, a ƙarƙashin shirin Transforming Education Systems at State Level (TESS), domin inganta sa ido da tabbatar da ingancin harkokin koyarwa.
Kwamishinan ma’aikatar ilimi a Jihar Katsina, Malam Yusuf Suleiman Jibiya, ne ya ƙaddamar da rabon baburan a ranar Litinin.
An rabawa daraktan sashen tabbatar da ingancin ilimi, daraktocin shiyyar tabbatar da ungancin ilimi guda 12, da jami’an tallafa wa makarantu guda 34 baburan domin sauƙaƙa musu gudanar da aikin sa ido a makarantu.
A jawabi sa a wajen taron, kwamishinan ya yaba wa Gwamna Dikko Umaru Raɗɗa bisa ci gaba da ba fannin ilimi muhimmanci da kuma zuba jari wajen inganta shi. Ya ce samar da baburan zai ƙara inganta sa ido da tabbatar da ingancin ilimi a makarantun jihar.
Ya tunatar da cewa a kwanakin baya Gwamna Raɗɗa ya ƙaddamar da rabon biliyoyin naira ga wasu makarantun firamare a ƙarƙashin shirin TESS domin aiwatar da ayyukan inganta makarantu, yana mai bayyana hakan a matsayin wani muhimmin mataki na bunƙasa ilimi.
Suleiman Jibiya ya kuma yaba wa mai kula da shirin TESS ta Jihar Katsina, Hajiya Binta Abdulmumin, bisa jajircewarta wajen gudanar da shirin. Ya umarci waɗanda suka amfana da baburan da su yi amfani da su ne kawai wajen ayyukan hukuma, musamman sa ido da duba yadda ake gudanar da harkokin koyarwa a makarantu.
Haka kuma, ya umarci sashen tabbatar da ingancin Ilimi da ya ƙara ƙaimi wajen kai ziyarar sa ido zuwa dukkan makarantu, har da waɗanda ke yankunan karkara. Ya kuma tabbatar da cewa ma’aikatar za ta gyara motocin gwamnati da suka lalace a wasu shiyyoyi domin ƙara inganta ayyukan sa ido.
Mai kula da shirin TESS ta Jihar Katsina, Hajiya Binta Abdulmumin, ta gode wa Gwamna Dikko Raɗɗa bisa cigaba da ba shirin goyon baya da kuma jajircewarsa wajen inganta ilimin firamare da sakandare a jihar.
A nasa jawabin, daraktan shiyyar tabbatar da ingancin ilimi na shiyyar Katsina, Alhaji Mujitapha Lawal, wanda ya yi magana a madadin waɗanda suka amfana, ya gode wa gwamnatin jihar tare da tabbatar da cewa za su yi amfani da baburan yadda ya kamata domin ƙarfafa sa ido kan makarantu da inganta ilimi a faɗin jihar.
