Majalisar dokokin Kano ta amince da ƙudirin kula da kuɗin karatu a makarantu masu zaman kansu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Litinin Majalisar Dokoki ta Jihar Kano ta kammala karatun ƙarshe akan ƙudirin kafa dokar kula da kuɗin karatu da ake biya a makarantu masu zaman kansu a faɗin jihar, inda ta samar da sababbin matakai da nufin bayar da kariya ga iyaye wajen biyan kuɗi sama da kima sakamakon ƙare-ƙare da kuma ƙarfafa matakin sanya ido a cibiyoyin ilimi.

Ƙudirin, wanda aka yi laƙabi da “Kano State Private and Voluntary Institutions Board (Amendment) Bill, 2026”, na neman a bunƙasa harkar kulawa da lamuran makarantu masu zaman kansu yayin tabbatar da tsare gaskiya da adalci da kuma inganta lamuran ci-gaban ilimi a baki ɗaya jihar.

Da yake jawabi, jagoran mafiya rinjaye, Lawan Hussaini ya ce gyaran zai wajabta wa makarantu firamare da sakandare na ƙudi wajen yin shawara da ƙungiyoyin iyaye da malamai (PTAs) kafin aiwatar da wani ƙarin kuɗin karatu.

Ya bayyana cewa, a ƙarƙashin sabuwar dokar, wajibi ne kowane ƙari da za a yi kada ya wuce kaso 10 na ainihin abin da ake karɓa a matsayin kuɗin karatu.

Haka kuma, ƙudirin dokar, wanda ke jiran sanya hannun Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar, ya hukunta cewa wajibi ne wanda zai riƙe muƙamin babban sakataren Hukumar kula da Makarantu masu Zaman kansu ya zama ma’aikaci mai ritaya ko wanda ya kai mataki na 14 a aikin gwamnati na fannin ilimi.

Ya ƙara da cewa, daga yanzu an haramta wa makarantun kuɗi cazar ɗalibai sama da kaso 10 na kuɗin jarrabawa da hukumomin jarrabawa kamar su WAEC, NECO da NBTE suka sanya.

Haka kuma, ƙudirin gyaran ya hukunta rage kuɗaɗen da makarantun kuɗi ke biyan hukumar kula da su daga kaso 15 zuwa biyar.

By Babaji

Leave a Reply