‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mutum shida a jihar Kaduna

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Yan bindiga sun yi garkuwa da mutum shida daga kauyen Hayin Gizo dake kusa da kauyen Garun Kurama a karamar hukumar Lere a jihar Kaduna a daren ranar Lahadi.

‘Yan bindiga sun shigo ƙauyen da ƙarfe 1:30 na dare inda ba su suka bar ƙauyen ba sai ƙarfe uku dare.

Maharan sun tafi da maza shida da mace ɗaya amma sai suka sake ta saboda rashin lafiyar da take fama da shi.

Wani majiyar da baya so a faɗi sunan sa ya bayyana cewa akwai Inyamurai biyu daga cikin mutum shida ɗin da aka yi garkuwa da su daga ƙauyen.

Ya yi kira ga jami’an tsaro da su gaggauta samar da tsaro a ƙauyen musamman yadda waɗanda aka yi garkuwa da su talakawa ne da ba za su iya biyan kuɗin fansa ba.

ƙananan hukumomin Lere, Kauru, Kachia, Zango Kataf, da Jema’a a cikin watanni da suka gabata na yawan fama da ayyukan ‘yan bindiga a yankinsu.

Bayan haka ‘yan bindiga sun kashe mutum biyu sannan mutum ɗaya ya ji rauni a ƙauyen Matsai dake ƙaramar hukumar Kaita a jihar Katsina.

Bisa ga sanarwar da Bakatsine ya saka a shafinta na ɗ dake yanar gizo ya nuna cewa maharan sun shigo ƙauyen a daren ranar Lahadi suna harbi ta ko ina inda garin haka ne suka kashe mutum biyu sannan mutum ɗaya ji rauni.

Sanarwar ya kuma ce maharan sun saci kaya masu darajar daga gidajen mutane a ƙauyen.

Zuwa lokacin da aka rubuta labarin rundunar ‘yan sandan ba su ce komai ba.

ƙaramar hukumar Kaita wace ke kusa da jamhuriyar Nijar na fama da hare-haren ‘yan bindiga a ‘yan shekarun nan.

By ukarofi