
Daga BELLO A. BABAJI
Rundunar ƴan sanda a Abuja, ta tabbatar da aukuwar wani hari da aka kai wa rukunin gadaje na Efab Global Estate da ke Idu a Industrial Area, wanda sama da ƴan bindiga 20 suka gudanar da raunata masu gadi biyar tare da yin fashi a gidaje da dama.
Wani shaida ya ce, ƴan fashin sun kai harin ne da tsakiyar dare, inda suka yi ta harbe-harbe domin tsorata al’ummar yankin.
Wani mazaunin unguwar ya ce, masu gadi biyar sun samu raunuka yayin da maharan suka yi fashi a gidaje shida, inda suka karɓe wayoyin hannu, kuɗaɗe, sarƙoƙi da wasu ababe masu daraja.
Kakakin rundunar ƴan sandan, Josephine Adeh ta bayyana cewa tuni aka fara gudanar da bincike domin farauto ƴan bindigar.
Ta kuma ce, sun ɗaure masu gadi guda biyu da raunata ɗaya, wanda daga bisani aka garzaya da shi Babban Asibitin Tarayya domin ba shi kulawa.
Haka kuma, kwamishinan ƴan sandan Abuja, CP Ajao Adewale ya yi kira ga mazauna da kwamitocin gudanarwa da su riƙa tabbatarwa da tantance waɗanda suke ɗauka aiki a matsayin masu gadi da ƴan aikin gida.
Har’ilayau, rundunar ta bada lambobi kamar haka domin bada rahoton duk wani abin zargi: 08032003913, 08028940883. 07057337653, da kuma na ƙorafi: 08107314192.
