Ƙungiyar daraktocin Najeriya (Directors’ Guild of Nigeria ) ta bayyana alhini da jimamin rasuwar Alhaji Umar Maikuɗi, wanda aka fi sani da Cashman, Shugaban ƙungiyar Motion Picture Practitioners Association of Nigeria (MOPPAN). A cewar sanarwar, rasuwar marigayin a ranar 21 ga Mayu, 2025 a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria ta bar babban giɓi a harkar fina-finan Najeriya.
An bayyana Cashman a matsayin jagora mai hangen nesa da jajircewa wajen inganta harkar fim a Najeriya.
Alhaji Maikuɗi ya kasance gwarzo da ya shahara wajen gina al’adu, inda ya yi fice wajen bunƙasa fina-finan harshen Hausa da kuma haɗa kan masana’antar fim a ƙasa baki ɗaya. Ayyukansa sun zama tushe ga ɗaruruwan masu shirya fina-finai, inda suka taimaka wajen wadata al’adun Najeriya da sabbin dabaru.
Gado da ya bari na zama gada tsakanin gargajiya da zamani zai ci gaba da karaɗe zukatan masu sana’a da masu kallo a ko’ina.
Ƙungiyar DGN, ƙarƙashin jagorancin Dr. Victor Okhai, ta miƙa ta’aziyya ga iyalan marigayin, abokan aikinsa a MOPPAN, da dukan al’ummar masu ƙirƙire-ƙirƙire. Sun bayyana cewa rayuwar shi abar koyi ce yayin da gudunmawar da ya bayar za ta ci gaba da haskaka hanyar waɗanda ya bari a baya.
