
Daga BELLO A. BABAJI
A ƙoƙarinsu na ɗinke barakar da ta mamaye jam’iyyar PDP, mambobin kwamiti na musamman kan sulhu a ƙarƙashin jagorancin tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki sun gana da Gwamnan Jihar Enugu kuma jagoran jam’iyyar a Kudu maso Gabas, Peter Mbah.
Sauran mambobin da suka halarci ganawar, wadda aka yi ta cikin sirri a Fadar gwamnatin jihar sun haɗa da tsofaffin gwamnonin jihohin Bayelsa da Gombe, wato Sanata Seriake Dickson da Ibrahim Ɗankwambo.
Bayan kammala zaman ne a yayin hira da manema labarai, Saraki ya ce sun yi zama da kwamitin sulhun ne don tabbatar da an gudanar da babban taron jam’iyyar na ƙasa da ke tafe cikin lumana ba tare da an samu wani tsaiko ba.
Ya kuma ce, Enugu ita ce jiha ta farko da suka ziyarta tun bayan kafa kwamitin nasu duba da rawar da yankin Kudu maso Gabas ke takawa ga jam’iyyar.
Haka kuma sun tattauna shawarwari musamman akan hanyoyin da za su taimaka wajen shawo kan matsalolin rarrabuwar kan ƴaƴan jam’iyyar da yadda za a magance faruwar irin haka a nan gaba gami da kawo ƙarshen rashin jituwan mambobinta.
