
Daga BELLO A. BABAJI
Rundunar ƴan sanda a Jihar Kaduna, ta kama wata mata mai suna Zaliha Shu’aibu bisa zargin ta da kashe jaririn abokiyar zaman ta mai watanni uku a Ķauyen Malari dake Ƙaramar Hukumar Soba a jihar.
Lamarin ya auku ne a ranar 13 ga watan Mayu, 2025 a gidansu inda ta ke tare da mijinta da kishiyar tata.
Kakakin ƴan sandan, Mansir Hassan ne ya faɗi hakan a wata takarda, ranar Juma’a, inda ya ce mahaifiyar jaririn mai suna Maryam Ibrahim, ta bar jaririn ne a lokacin da ta shiga makewayi domin biyan wata buƙata.
Bayan ta dawo ne ta samu wadda ake zargin tare da jaririn ciki mawuyacin hali inda ta ga kumfa na fita a bakinsa da wani rauni a wuyansa, lamarun da suka yi sanadin mutuwarsa bayan garzayawa da shi wani asibiti a ķauyen.
Kakakin ƴan sandan ya bayyana cewa, bayan gudanar da bincike mai zurfi ne aka gano cewa Zaliha tare da ƙanin mijinta, Lawal Muhammad ne suka kitsa makircin, inda ta furta cewa da sinadarin asid ta yi amfani wajen halaka jaririn.
Kwamishinan ƴan sandan jihar, Rabi’u Muhammad ya tabbatar wa al’umma cewa, za a yi adalci a yayin hukunci game da al’amarin.
