‘Yan bindiga sun yi garkuwa da Shugaban Ƙaramar Hukumar Keffi

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

Yan bindiga sun yi garkuwa da Shugaban Ƙaramar Hukumar Keffi, Hon Baba Shehu a kan hanyarsa ta komowa Keffi daga Lafia babban birnin jihar Nasarawa.

Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Juma’a inda maharan suka yi awon gaba da Shugaban Karamar Hukumar tare da direbansa, Mohamme Tanimu (Senior Man).

Sai dai dogarin Shugaban Karamar Hukumar, Alhassan Habeeb, ya rasa ransa sakamakon harbin bindiga yayin harin.

Da safiyar Asabar aka yi jana’izar marigayi Habeeb a Keffi kamar yadda Addinin Musulunci ya tanada.

Ya zuwa haɗa wannan labari, maharan sun buƙaci a biya su miliyan N30 kafin su sako mutum biyun da suke riƙe da su.

By Editor