Yau Zamfara za ta karɓi baƙuncin Osinbajo

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau

Gwamnatin jihar Zamfara da Jam’iyyar APC reshen jihar sun shirya tsaf domin tarbar Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo a wani ɓangare na rangadin da yake yi a jihohi.

A yayin ziyarar tasa, ana sa ran Osinbajo zai gana da wakilan jihar da sarakuna 19 da ma Gwamnan Jihar, Bello Mohammed Matawalle.

Jaridar Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa, an baza jami’an tsaro daban-daban a sassan Gusau, babban birnin jihar domin tabbatar da ziyarar da Mataimakin Shugaban Ƙasar zai yi an kammala ta cikin kwanciyar hankali.

Ana sa ran Osinbanjo ya isa Gusau da ƙarfe 2:30 na yau Adabar.

By Editor