Rundunar sojin Nijeriya ta yi watsi da zargin cinye alawus ɗin ƙananan sojoji

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Rundunar sojin Nijeriya ta yi watsi da wani zargi na cin hanci da rashawa da wasu manyan sojojin ke yi.

Sojojin sun yi kukan cewa manyansu na cinye musu kuɗaɗensu na alawus, inda suka buƙaci Shugaba Buhari ya ɗauki mataki a kai, idan ba haka ba za su yi bore.

Jami’an sun zargi manyansu da cinye musu kuɗaɗensu na alawus.

Rundunar sojin ta bayyana cewa tana aiki ne da tsarin biyan albashi na bai-ɗaya ta intanet da gwamnati ta fito da shi, kuma abin da take yi ba shi da bambanci da wanda takwarorinta, da sojin sama da na ruwa ke yi, don haka a cewar rundunar babu yadda za a zalunci wani a ƙarƙashin tsarin.

Wani abin da rundunar ta ce yana da tayar da hankali shi ne barazanar da ƙananan sojojin suka yi cewa za su yi yajin aiki idan ba a biya su haƙƙoƙinsu ba, alhali a irin wannan yajin aikin a aikin ɗamara tamkar tawaye ne ko bore ga ƙasa.

Wata sanarwar da daraktan hulɗa da jama`a na sojin ƙasan Nijeriya, Birgediya-janar Onyema Nwachukwu ya sanya wa hannu ta ce zargin da sojojin ke yi ya nuna cewa sun jahilci yadda soji ke tafiyar da harkar kuɗi.

Ya tabbatar da cewa ana zargin ne da nufin ɓata wa sojin ƙasa suna tare da sanyaya gwiwar dakarunta, waɗanda ta ce sabon Hafsansu ya dawo da armashi da karsashin aikin a zukatan zaratan ƙasar sakamakon yadda ake biya musu haƙƙoƙinsu.

Kazalika rundunar ta lura cewa sojojin sun yi zargin ne a cikin wata kurmar wasiƙa, wadda suka aike wa Shugaba Buhari ba tare da an rubuta sunayen masu ita ba, wadda hakan a cewar rundunar alama ce ta rashin gaskiya.

Amma duk da haka, rundunar sojin ta ce za ta gudanar da bincike a kan lamarin.

Ƙananan sojojin dai sun rubuta buɗaɗɗiyar wasiƙa ne zuwa ga Shugaba Buhari, wadda a ciki suka zargi manyan sojin Nijeriya da yi musu ƙwange, kuma sun kwana biyu suna kokawa amma shugaban ƙasar da sauran waɗanda abin ya shafa basu ce komai ba.

A cikin wasiƙar, sojojin suka ce kuɗaɗensu na alawus daban-daban ba sa shiga hannunsu, har ta kai ga su suke ƙuƙutawa su saya wa kansu takalma da sauran kayan ɗamara.

Sojojin sun bayyana cewa duk da cewa wasu na raina su ba don sadaukar da rayukansu da suke yi ba da komai ya cije a Nijeriya.

Sun yi gargaɗin cewa idan tura ta kai bango, har suka yi tawaye, to manyan sojojin da suke musu cogen za su rasa inda za su sa kansu da ‘ya’yansu.

Haka kuma za su rasa inda za su tsuguna su ci abin da suka tara. Sannan za su rasa hanyar da za su fice daga Nijeriya.

Babu wani martanin da ya fito daga fadar shugaban na Nijeriya dangane da wannan buɗaɗɗiyar wasiƙar.

By Editor