Daga ABUBAKAR A. BOLARI a Gombe
Sarkin Dawakin Sarkin Bajoga Alhaji Bello Adamu ya naɗa masu sarautun gargajiya 18 ciki har da Sufeton ‘yan sanda, Abdulkareem Abubakar a matsayin garkuwansa.
A lokacin bikin naɗin sarautar, Sa’in Funakaye Alhaji Umar Abdulsalam Baciji, ya yaba wa Sarkin Dawakin Bajoga na yadda ya zaɓo haziƙan matasa ‘yan Boko da ‘yan kasuwa da ma’aikatan gwamnati ya ba su sarautu daban-daban don ciyar da masarauta gaba.
Sa’in Funakaye, ya ce hakan zai ƙara wa masarauta da sarakuna wanda sune ke da jini a jiki da za su iya gudanar da duk abinda ake so akan lokaci.
Da yake jawabin godiya Sarkin Dawakin Bajoga, Alhaji Bello Adamu Bajoga, ya gode wa mai martaba Sarkin Bajoga da ya ba shi dama na gudanar da naɗe-naɗen don jan matasan a jiki.
Ya kuma yi amfani da damar ya jinjina wa mai martaba Sarkin Gombe Alhaji Abubakar Shehu Abubakar, III kasancewar shugaban majalisar sarakuna na jihar Gombe kuma yana tafiya da kowa ba tare da kyama ba, wanda hakan tasa suke koyi da halayensa kyawawa.
Ɗaya daga cikin waɗanda aka naɗa ɗin Garkuwan Sarkin Dawakin Sufeton ‘yan sanda Abdulkareem Abubakar, da yake zantawa da wakilin mu cewa ya yi sarautar gargajiya ita ce tushen koyar da ɗa’a da tarbiyya, kuma sai aka yi sa’a dukkan su matasa ne masu tasowa wanda wannan sarautar za ta ƙara koya musu yadda ake mu’amula da mutane.
Sufeto Abdulkareem, ya kirayi matasa da su yi koyi da ɗabi’ar Sarkin Dawaki wanda ya ce shigowar su harkar sarauta zai kare su daga shiga aika-aikar miyagu.
Garkuwan, ya ƙara da cewa rashin jan matasa a jiki shi ya haifar da yawan ayyukan ta’addanci wanda masu aikatawar duk matasa ne.
Daga nan sai ya ja hankakin al’umma na su dinga bai wa masarautu da sarakuna haɗin kai da goyon baya a matsayin su na iyayen ƙasa.
Bikin ya ƙayatar, inda aka yi bushe-bushe da kaɗe-kaɗe na al’ada, kana aka gudanar da ƙwarya-kwaryar hawan daba.
