‘
Daga UMAR GARBA a Katsina
Balan Auwal, wani babban ɗan kasuwa a Jihar Katsina ya rasa ransa a hannun ‘yan bindiga, makonni bayan da ɓarayin suka yi garkuwa da shi tare da ɗansa.
An yi garkuwa da Auwal ne a ranar 26 ga Fabrairu, 2025, lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai hari garin Malumfashi da ke jihar Katsina, ban sun yi harbi kan mai uwa da wabi.
Majiyar Blueprint Manhaja ta bayyana cewa duk da an yi artabu tsakanin ‘yan bindingar da kuma jami’an tsaro a lokacin harin wanda aka kai da dare, ‘yan ta’addan sun yi nasarar tserewa da Auwal tare da ɗansa, mai suna Saifullahi.
Rahotanni sun ce an yi ƙoƙarin ganin an sako su, amma a ranar Lahadi, wani mai sharhi kan harkokin tsaro da ake kira Bakatsine ya tabbatar da mutuwar ɗan kasuwa Alhaji Auwal.
“Alhaji Balan Auwal Mai Gwanjo na ƙaramar hukumar Malumfashi,
Jihar Katsina, ya rasu a hannun ‘yan bindiga bayan da ya shafe makonni a hannun ‘yan bindingar ” Inji Bakatsine.
