Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Uwargidan shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, Sanata Oluremi Tinubu, ta ƙaddamar da shirin noma a gida ga mata 60 a Jihar Zamfara wanda shiri ne na sana’ar noma ga mata.
Da take jawabi a madadin uwargidan shugaban ƙasar a wajen taron, uwargidan gwamnan jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta bayyana cewa shirin yana ƙarƙashin shirin Renewed Hope Initiative ne na uwargidan shugaban ƙasar tarayyar Najeriya, Sanata Oluremi Tinubu tare da haɗin gwiwar ma’aikatar noma da samar da abinci ta tarayya.
Hajiya Huriyya Dauda Lawal ta ci gaba da cewa shirin an tsara shi ne domin yaƙar yunwa a tsakanin matan aure.
“Ta hanyar noma ƙananan kayan gona a gida, za mu iya ciyar da iyalanmu, mu tallafa wa al’ummominmu, da samar da kuɗin shiga ta hanyar rarar kayan amfanin gonan da muka noma.” Ta ce
“Wannan shiri ba wai kawai game da shuka amfanin gona bane harma da samar da abinci ga kowa da kowa”. Ta ce
Ta kuma ci gaba da cewa, kowane wanda ya ci gajiyar shirin zai samu cikakken taki, iri, abun ban ruwa, fartanya da tallafin kuɗi naira 200,000.
Hajiya Huriyya ta buƙaci matan Jihar Zamfara da su ɗauki shirin da muhimmanci, su yi koyi da shi, sannan su koya wa ‘ya’yansu mata.
“Ta hanyar sanya noma wani ɓangare na rayuwarmu ta yau da kullun, za mu iya tabbatar da cewa babu iyali da ke fama da yunwa”. Ta ƙara da cewa
Daga nan, uwargidan gwamnan Jihar Zamfara ta yabawa uwargidan shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, Sanata Oluremi Tinubu bisa ƙaddamar da wannan shiri na hangen nesa a jihar.
A cewarta, shirin zai taimaka wajen yaƙar fatara da samar da ayyukan yi a tsakanin mata a gidajen aurensu da ke jihar.
