
Daga BELLO A. BABAJI
Rahotanni daga Jihar Ondo a Kudu masu yammacin Nijeriya, sun bayyana cewa an yin garkuwa da wani jigon jam’iyyar APC mai suna Nelson Adepoyigi.
Lamarin ya auku ne a yankin Ifon dake Karamar Hukumar Ose a jihar.
Rundunar ƴan sandan jihar ta tabbatar da faruwar al’amarin, inda ta ce wasu ƴan bindiga sun yi garkuwa da Adepoyigi, wanda shi ne shugaban APC a gundumar Ifon a gidansa dake yankin, ranar Litinin.
Kakakin ƴan sandan, Olushola Ayanlade ya ce an sace ďan siyasar ne a daidai mashigar gonarsa.
Haka kuma ya ce, DPO’n Ifon da haďin-gwiwar mafarauta da ƴan bijilante da sojoji sun kaddamar da atisayen farauto waɗanda ake zargi da aikata laifin.
